Rikicin PDP: Bayan Ganawa Da Tinubu, Sanatan Arewa Ya Aika Da Sako Mai Muhimmanci Ga Wike Ga Gwamonin G5

Rikicin PDP: Bayan Ganawa Da Tinubu, Sanatan Arewa Ya Aika Da Sako Mai Muhimmanci Ga Wike Ga Gwamonin G5

  • Bayan taron da aka rahoto cewa gwamna Wike da magoya bayansa sun yi a kasar waje, an bukaci su yi abin da ya dace
  • Hakan na zuwa ne yayin da tsohon sanatan Kaduna, Shehu Sani ya bukaci gwamnonin na G5 su goyi bayan Atiku Abubakar gabanin zaben 2023
  • A bangare guda, gwamnonin da ke fushi da PDP sun gana da Bola Tinubu na APC, sun ce yana cikin tattaunawa da suka yi da masu ruwa da tsaki

Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya kuma jigon jam'iyyar PDP, Sanata Shehu Sani, ya bukaci gwamnonin G5 su hakura su goyi bayan dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar don ya ci zaben 2023.

G5 din karkashin jagorancin Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, ta hada da gwamononi kamar haka; Samuel Ortom (Benue), Seyi Makinde (Oyo), Okezie Ikpeazu (Abia) da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu).

Kara karanta wannan

Ganawar sirri: Daga karshe bayani ya fito bayan ganawar Tinubu da gwamnonin PDP 5 a Landan

Gwamnonin G5
Rikicin PDP: Bayan Ganawa Da Tinubu, Sanatan Arewa Ya Aika Da Sako Mai Muhimmanci Ga Wike Ga Gwamonin G5. Hoto: Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sani ya shawarci Wike da sauran gwamnonin G-5

Sun samu matsala da Atiku ne kan batun rashin mayar da shugabancin jam'iyyar na kasa zuwa yankin kudu bayan dan takarar shugaban kasa ya fito daga arewa.

A hirar da The Guardian ta yi da shi a Kaduna, a ranar Laraba, 28 ga watan Disamba, shugaban kungiyar kare hakkin bil adama na Civil Rights Congress of Nigeria (CRCN), Sani, ya ce idan har nan da sati biyu ba a daidaita tsakanin gwamnonin biyar da Atiku ba, ba za a taba yin sulhu ba.

A cewar Sani, matsalar siyasan tsakanin gwamnonin PDP din na G-5 da Atiku ya dade, yana mai cewa lokaci ya yi da za su hakura su yi sulhu don nasarar PDP a zaben shekara mai zuwa.

Kara karanta wannan

Asalin Abin da Ya Sa Gwamnonin PDP Suka Hadu da Tawagar Tinubu Ta Bayyana

Mai rajin kare hakkin biladaman ya fada wa jaridar cewa gwamnonin na G-5 na daf da ruguza siyarsu, idan suka goyi bayan dan takarar wata jam'iyyar a gaba, yana mai cewa shedanin da ka sani ya fi wanda ba ka sani ba.

Ya ce:

"Gwamnonin G5 su mayar da takkubansu su goyi bayan Atiku Abubakar. Gara shedanin da ka sani da wanda baka sani ba. Duk inda suka tafi, za su zama baki ne, kuma duk wanda ya ci zabe idan ba Atiku ba, ba zai fifita su kan mutanen da suka dade tare da shi ba."

Sani ya gargadi Wike, gwamnonin G-5 kan taro da Tinubu

Ya gargade su da suyi takatsantsan su sani cewa babu wanda zai iya kare su fiye da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar su.

Yayin da Wike ya ce zai bayyana dan takarar shugaban kasa da zai goyi baya a Janairu, gwamnonin na G5 sun tafi Landan, watakila don cimma matsaya kan dan takarar shugaban kasa da za su mara wa baya.

Kara karanta wannan

2023: Dan Takarar Gwamna da Wasu Kusoshin APC Sama da 500 Sun Koma PDP, Abokin Gamin Atiku Ya Magantu

Bayani ya fito bayan rahoton cewa Tinubu ya gana da gwamonin G-5 a Landan

Gwamnonin da ke fushi da jam'iyyar PDP wato G5 sun gana da dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu a Landan.

Punch ta rahoto cewa Tinubu na kokarin shawo kan gwamnonin ne don su mara basa baya a babban zaben 2023 a ganawarsu ta ranar Talata 27 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel