Bayani Ya Fito Bayan Rahotanni da Ke Cewa Gwamnonin G5 Sun Gana da Tinubu a Landan

Bayani Ya Fito Bayan Rahotanni da Ke Cewa Gwamnonin G5 Sun Gana da Tinubu a Landan

  • Kacaniyar siyasa a Najeriya gabanin zaben 2023 ta sake daukar sabon salo yayin da gwamnonin G-5 na PDP suka gaNa da Tinubu a Landan
  • A cewar wata majiya, gwamnonin na PDP biyar masu fushi da jam’iyyarsu sun ce goyi bayan kowane dan takarar shugaban kasa ba
  • A tun farko gwamnonin G-5 sun barranta da Atiku ne saboda rikicin cikin gida da ya barke bayan zaben fidda gwanin shugaban kasa

Landan, Burtaniya – Gwamnonin G-5 na PDP masu fushi da uwa jam’iyya sun gana da dan takarar shugaban kasan jam’iyya mai ci ta APC; Bola Ahmad Tinubu a birnin Landan.

A cewar rahoton Punch, Tinubu na siyan baki don lashe zukatan gwamnonin na G-5 don kawai su goyi bayansa a zaben 2023 mai zuwa, saboda haka suka hadu a ranar Talata 27 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Asalin Abin da Ya Sa Gwamnonin PDP Suka Hadu da Tawagar Tinubu Ta Bayyana

Legit.ng ta tattaro cewa, gwamnonin biyar daga Kudu sun gama kai don ganin sun tumbuke dashen tushen Iyorchia Ayu da ke kan kujerar shugabancin PDP, kuma sun ce tumbuke shi a kujerar ne zai sa su marawa Atiku baya a 2023.

Bayanai sun fito na ganawar Tinubu da gwanonin G-5
Bayani Ya Fito Bayan Rahotanni da Ke Cewa Gwamnonin G5 Sun Gana da Tinubu a Landan | Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Gov Nyesom Ezenwo Wike - CON
Asali: Facebook

Gwamnonin dai sanannu ne, su ne; Nyesom Wike, Seyi Makinde, Okezie Ikpeazu, Samuel Ortom da Ifeanyi Ugwuanyi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meye ya faru bayan ganawar Tinubu da gwamnonin G-5?

Pulse ta tattaro cewa, majiya ta yi karim haske game da wannan ganawa, inda tace:

“Tinubu ya gana da fusatattun gwamnonin jiya (Talata) tare da wakilcin jama’ar da suka hada (Kayode) Fayemi, (Babajide) Sanwo-Olu da wani gwamna mai ci da kuma tsohon gwamna.
“Yanzu dai, muna jiran gwamnonin na G-5 ne su bayyana a hukumance a cikin watan Janairu.”

Meye gwmanonin suka bukata daga Tinubu?

Kara karanta wannan

Sanatan PDP Mai Goyon Bayan Tinubu Ya Gana da Kwamitin Yakin Neman Zaben APC

Duk da cewa majiyar bata bayyana karara kan abin da suke bukata ba cewa ba za ta yi sakin baki ba, ta ce shugabannin na PDP sun bayyana ganawar cewa, ba sa goyon bayan kowane dan takarar shugaban kasa.

A cewar majiyar:

“Bani da karin bayani game da hakan. Abin da na sani shine cewa sun gana kuma sun bayyana a ganawar cewa ba sa goyon bayan kowane dan takara.”

Wani batu mai rikitarwa

Har ila yau, batun bai tabbatar gwamnan Legas da Fayemi sun halarci ganawar ba kamar yadda majiyar ta bayyana.

“Na sami kiraye-kiraye da yawa game da rahoton tafiyar gwamnan tare tare da Asiwaju (Tinubu) kuma zan iya ce muku har yanzu yana nan a Najeriya.
“Bal ma, na yi magana dashi a yau (Laraba) har sau biyu. Idan ma zai yi don ganawa da gwamnonin G-5 a wajen kasar, ba abu ne da zai so ya bayyana ba, amma tabbas yana nan a kasar nan.”

Kara karanta wannan

Sabon salo: 'Ya'yan Buhari za su taya matasan Najeriya tallata Tinubu da APC gabanin 2023

Gwamnonin sun ce, wannan fafutuka da suke ba iya a zaben 2023 zai tsaya ba, fafutuka ce da za ta kai har bayan babban zaben na badi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel