'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Ofishin INEC Na Jihar Imo, An Kashe Uku Daga Cikinsu

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Ofishin INEC Na Jihar Imo, An Kashe Uku Daga Cikinsu

  • Rundunar 'yan sandan jihar Imo sun yi nasarar fatattakar 'yan bindigan da suka kai wani mummunan hari kan ofishin INEC
  • An kone wani yanki daga ofishin na INEC da ke birnin Owerri, lamarin da ya jawo tashin hankali
  • Ana ci gaba da samun hare-hare kan ofisoshin INEC musamman a yankunan Kudu, tsoro na shiga zukatan masu kada kuri'u

Owerri, jihar Imo - Da sanyin safiyar yau Litinin 12 ga watan Disamba ne 'yan bindiga suka kai mummunan hari kan ofishin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) a Owerri, babban birnin jihar Imo.

An ruwaito cewa, sun lalata wani bangare na ginin yayin da suka dasa bam da ya tashi a wurin, jaridar rahoton Punch.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Mike Abattam ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce an hallaka 'yan bindigan uku yayin da aka kwato kayan fashe daga hannunsu.

Kara karanta wannan

Babbar magana: 'Yan kwamitin yaki da 'yan daba sun rusa ofishin kamfen APC a jihar APC a Arewa

An kone ofishin INEC
'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Ofishin INEC Na Jihar Imo, An Kashe Uku Daga Cikinsu | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wannan na zuwa kwanaki takwas kenan bayan da aka kone wani ofishin INEC a kamarar hukumar Orlu ta jihar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani yanayin, 'yan bindiga sun yi irin wannan barna kan ofishin INEC a jihohin Ebonyi, Osun da Ogun a cikin kasa da makwanni hudu kacal.

Wannan lamari dai ya fara ba masu kada kuri'u a Najeriya tsoro yayin da ake fuskantar babban zaben 2023 mai zuwa nan da watanni kasa da uku.

Yadda harin ranar Litinin ya auku

Sabon harin na Owerri, wanda aka kai da misalin karfe 3 na safe, ya zo da tasgaro ga 'yan bindigan, domin uku sun hallaka, ciki har da wani babban kwamandansu.

Hakazalika, an kwato bindigogi AK47 da wasu kananan bindigogi kana da ababen hawa takwas daga hannun 'yan bindigan.

Wata majiya ta bayyana cewa:

Kara karanta wannan

Bayan Kashe Ma'kudan Ku'da'de Wajen Gina Gada, Yanzu Dai Gadar Ta Fara Tsagewa

"Da sanyin safiyar nan, 'yan bindiga sun kai mummunan hari kan ofishin INEC na Owerri, a jihar Imo amma gamayyar jami'an tsaro sun yi nasarar dakile harin kana suka kashe uku daga cikinsu, ciki har da kwamandansu.
"An kwato ababen hawa guda bakwai, ciki har da AK47 guda bakwai da kuma wasu bindigogi. Da yawan 'yan bindigan sun tsere da raunukan harbin bindiga. Amma an kone motar 'yan sanda guda daya."

AK47 uku aka kwato ba bakwai ba, inji 'yan sanda

Sai dai, a nasa bangaren, Abattam ya ce bindigogi guda uku kacal akwa kwato AK47 da kuma wasu ababen hawa, rahoton Vanguard.

A cewarsa:

"Mun kashe uku daga cikin wadanda suka kawo harin kuma mun kwace bingogi AK47 guda uku da wasu kananan bindigogi. Mun kwato kayan fashewa da uku daga cikin abin hawansu."

An tattaro cewa, lamarin tsaro na ci gaba da yin tsami a Owerri tun bayan faruwar harin.

Kara karanta wannan

Iyalai A Nigeria Na Hakura Da Ci Su Koshi Sabida Yanayin Tashin abinci

Wani mummunan hari da aka kai Orlu ya jawo tsoro a jihar Imo, inda aka kone ofishin INEC kurmus ana tsaka da shirin yin zabe badi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel