Ta Faru Ta Kare, Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Halascin Takarar Gwamnan APC a 2023

Ta Faru Ta Kare, Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Halascin Takarar Gwamnan APC a 2023

  • Kotun Koli da ake wa lakabi da daga ke sai Allah ya isa ta kawo karshen takaddama kan tikitin takarar Sanatan Ebonyi ta kudu a APC
  • An kai ruwa rana tsakanin Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi da kuma Princess Ann Agom-Eze, wacce ta zo ta 2 a zaben fidda gwani
  • Bayan gwamnan ya rasa tikitin shugaban ƙasa, kaninsa wanda ya samu tikitin Sanata a mazaɓar ya sadaukar da takararsa ga Umahi

Abuja - Kotun Ƙoli a Najeriya ranar Jumu'a ta tabbatar da gwamna David Umahi a matsayin halastaccen ɗan takarar Sanatan jam'iyyar APC a mazaɓar Ebonyi ta kudu.

Yayin yanke hukunci, kwamitin alƙalai biyar bisa jagorancin mai shari'a Kudirat Ekekere-Ekun ta kori ƙarar da 'yar takarar Sanatan mazaɓar, Princess Ann Agom-Eze ta shigar.

Gwamna Dave Umahi na jihar Ebonyi.
Ta Faru Ta Kare, Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Halascin Takarar Gwamnan APC a 2023 Hoto: Dave Umahi
Asali: UGC

Channels tv tace Kwamitin Alkalan sun yanke cewa karar da fusatacciyar 'yar takarar ta ɗaukaka zuwa Kotun ba ta dace ba sam kuma ya kamata a yi fatali da ƙorafin.

Kara karanta wannan

2023: Babbar Kotu Ta Kori Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Wata Jiha

Yadda aka kai ruwa rana kan tikitin Sanatan Ebonyi ta kudu

Mista Agom-eze ce ta zo ma biyu a zaɓen fidda gwanin da jam'iyyar APC ta shirya a mazaɓar ranar 28 ga watan Mayu, 2022, wanda Austin Umahi, ƙanin gwamna Umahi ya samu nasara.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai bayan gwamnan ya sha ƙasa a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC, ƙaninsa bisa ra'ayin kansa ya ce ya sadaukar da tikitinsa na Sanata ga yayansa watau gwamna Umahi.

Bayan haka hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), yayin da ta nuna rashin gamsuwa da batun, ta sanar da cewa ba zata amince da takarar gwamnan ba.

Haka zalika bayan, Misis Agom-Aze ta shigar da ƙara, babbar Kotun tarayya mai zama a Abakaliki ta soke takarar David Umahi kuma ta umarci jam'iyyar APC ta shirya sabon zaɓe a mazaɓar cikin kwanaki 14.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-dumi: Babbar Kotu Ta Rushe Dukkanin Zabukan Fidda Gwanin PDP a Wata Jiha

Domin biyayya ga wannan umarni, APC ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani ranar 31 ga watan Yuni, 2022 kuma gwamna Umahi ya samu nasarar lashe tikitin.

Duk da haka bata yarda ba, Agom-Eze, ta garzaya Kotu tana neman a soke matakin APC na canza zaɓe, ƙarar da babbar Kotu da Kotun ɗaukaka ƙara suka yi fatali da ita, a cewarsu babu dalilin soke ingancin sabon zaben.

Kotun Koli ta kawo ƙarshen taƙaddama

Daga ƙarshe The Cable ta tattaro cewa a ranar Jumu'a 9 ga watan Disamba, Ƙotun Allah ya isa ta amince da sabon zaɓen fidda gwanin kana ta ayyana gwamna Umahi a matsayin sahihin ɗan takara.

Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Halascin Takarar Tinubu a 2023

A wani labarin kuma Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta kawo karshen ƙarar da aka shigar don soke takarar Bola Tinubu a zaɓen 2023

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Samu Karin Karfi, Ɗan Takarar Gwamna a Wata Jam'iyya Ya Koma PDP

A wata sanarwa da mai magana da yawun kwamitin kamfen APC, Bayo Onanuga ya fitar, yace Kotun ta yi watsi da ƙarar, tace wanda ya shigar ba shi da hurumin ƙalubalantar Tinubu.

Wannan dai ita ce ƙara ta hudu da Kotu ta sallama kan Tinubu ciki har ƙarar da jam'iyyar AA da wasu mutane suka shigar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel