Satar Kudin Kananan Hukumomi: Gwamnan Kudu Mai Karfin Fada A Ji Ya Gargadi Buhari

Satar Kudin Kananan Hukumomi: Gwamnan Kudu Mai Karfin Fada A Ji Ya Gargadi Buhari

  • An gargadi Shugaba Muhammadu Buhari game da yi wa gwamnoni kudin goro
  • Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a ranar Juma'a 2 ga watan Disamba ne ya yi wa Shugaban kasar wannan gargadin
  • A cewar gwamnan, abin takaici ne yadda shugaban kasar ya zargi gwamnonin da satar kudin kananan hukumomi ba tare da fayyace wa ba

Gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya nesanta kansa daga shugabanni masu satar kudaden kananan hukumomi.

Da ya ke martani kan zargin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi cewa gwamnoni da yawa sun kware wurin satar kudaden kananan hukumomi, Okowa ya ce baya cikin masu satar kudin.

Okowa da Buhari
Satar Kudin Kananan Hukumomi: Gwamnan Kudu Mai Karfin Fada A Ji Ya Gargadi Buhari. Hoto: Delta Government, Muhammadu Buhari.
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan, wanda kuma shine dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023 ya ce abin takaici ne shugaban kasar zai yi irin wannan ba tare da fayyacewa ba.

Kara karanta wannan

Karyane: Gwamnoni 36 sun yi martani, sun fadi yadda Buhari ya jefa Najeriya cikin talauci

Sanarwar da sakataren watsa labarai na Okowa, Olisa Ifeajika, ya fitar, ya ce Buhari a matsayinsa na shugaban kasa ya san gwamnoni masu irin wannan abin.

Ya kara da cewa a maimakon yin 'magana na gaba daya' ana sa ran shugaban kasar ne ya fitar da sunayen masu aikata hakan.

Kalamansa:

"Ina son in ce shugaban kasa, a matsayinsa na wanda ke da dukkan bayanai kan kasar ya san gwamnonin da suke rukunin wadanda ya ke nufi da 'barayi'.
"Dukkan mu mun san gwamnan mu, Dr Ifeanyi Okowa, baya cikin masu aikata hakan. Yana daga cikin gwamnonin farko, idan ba ma na farko ba, da ya rungumi bada yancin kananan hukumomi lokacin da aka amince da hakan kuma ya yi wa bangaren shari'a da majalisa."

Obasanjo ya koka kan gazawar Najeriya na bunkasa kanta a matsayin jigon Afirka

Olusegun Obasanjo ya ce baya jin dadin yadda abubuwa ke faruwa da tattalin arzikin Najeriya da mutanen kasar.

Kara karanta wannan

Daya Bayan Daya, Gwamnoni Suna Maidawa Buhari Martanin Zargin da Yayi Masu

Tsohon shugaban kasar ya ce kasar na cigaba da bawa duniya da Afirka kunya ta hanyar rashin kai matakin da ya dace ace ta kai.

A cewar Obasanjo, akwai bukatar shugabannin kasar da yan Najeriya su yi amfani da albarkatun da kasar ke da shi.

Gwamnonin PDP 2 Sun KallubalanciBuhari Kan Zargin Gwamnoni Da Satar Kudin Kananan Hukumomi

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da takwararsa Samuel Ortom na jihar Benue sun kallubalanci shugaba Buhari ya fallasa gwamnonin da ya ce suna sace kudaden kananan hukumomi

Gwamnonin na kungiyar G5 su kallubalanci Buhari a ranar Juma'a a lokacin kaddamar da aikin titi na Mgbuosimini a jihar Ribas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel