Zaben 2023: Muna Maka Fatan Alkhairi, APC Ga Babachir Bayan Ya Sha Alwashin Goyon Bayan Atiku

Zaben 2023: Muna Maka Fatan Alkhairi, APC Ga Babachir Bayan Ya Sha Alwashin Goyon Bayan Atiku

  • Jam'iyyar APC ta yiwa Babachir Lawal fatan alkhairi a yunkurinsa na marawa Atiku Abubakar baya a zaben 2023
  • Lawal wanda jigo ne na APC kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya ce har yanzu shi dan jam'iyyar ne amma ba zai marawa Bola Tinubu baya ba
  • Sai dai jam'iyyar mai mulki ta ce kuri'a daya kawai zai iya kadawa a zaben

Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi martani ga alwashin da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya dauka na zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratin Party (PDP), Atiku Abubakar.

Kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto, Lawal ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar, ya yarda da abun da kiristocin arewa ke so kuma zai samu cikakken goyon bayansa.

Kara karanta wannan

2023: Dan majalisa a APC ya ba 'yan Najeriya wata shawara kan zaban Tinubu

Tinubu
Zaben 2023: Muna Maka Fatan Alkhairi, APC Ga Babachir Bayan Ya Sha Alwashin Goyon Bayan Atiku Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

A wani sako da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ta saki ta hannun kakakinta, Festus Keyamo, jam'iyyar mai mulki ta yi watsi da barazanar Babachir.

Keyamo ya ce bai ga ta inda Lawal, wanda ya kasa kawo mazabarsa a zabukan baya zai iya hana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu cin zabe a 2023 ba, jaridar Punch ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake bayyana cewa Lawal na da iko ne kan kuri'a daya a zaben, Keyamo ya ce APC na yiwa tsohon sakataren gwamnatin tarayyan fatan alkhairi a yunkurinsa.

Keyamo ya ce:

"Muna yi masa fatan alkhairi. Yana da yancin yanke wata shawara. Amma a matsayinmu na tawagar kamfen din jam'iyyar, mun ci gaba da harkokinmu. Yana da yancin kuri'a daya ne kawai.
"Ban san kimai game da mabiyansa ba. Amma hakan bai ma taimake shi wajen lashe mazabarsa ba a zabukan 2015 da 2019."

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi da Musulmi: Tinubu Da Shettima Ba Za Su Dandana Mulkin Najeriya Ba a 2023, inji Babachir Lawal

Tinubu ba zai ci zaben 2023 ba, Babachir

A baya mun ji cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya ce tikitin Musulmi da Musulmi da jam'iyyar APC ta yanke shawarar yi babban zaben 2023 zai hana ta kawo kujerar shugaban kasa.

A hirarsa da sashin BBC, tsohon SGF din ya ce shi dai ba zai taba yin Tinubu ba zabe mai zuwa inda yayi zargin cewa an yaudaresu su kiristocin arewa don ba a ganinsu da gashin kai.

Babachir ya ce yanzu haka suna tattaunawa da babbar jam'iyyar adawar kasar don dinkewa a kokarinsu na ganin Alhaji Atiku Abubakar ya yi nasara wajen kayar da Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel