2023: Tinubu Ba Zai Ba ’Yan Najeriya Kunya Ba, Dan Majalisa

2023: Tinubu Ba Zai Ba ’Yan Najeriya Kunya Ba, Dan Majalisa

  • Mamban majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar Ondo ta Gabas ya magantu kan yadda Tinubu zai yi mulkinsa bayan 2023
  • Ya ce sam dan takarar shugaban kasan na APC ba zai ba 'yan Najeriya kunya ba matukar aka zabe shi a zaben 2023
  • Ya kuma bayyana cewa, Tinubu ya kafa tarihi a Legas, kuma zai yi irin hakan idan aka zabe shi ya gaji Buhari

Jigar Ondo - Mamban majalisar wakilai ta kasa daga Ondo ta Gabas, Abiola Makinde ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ba zai ba 'yan kasar nan kunya ba.

Ya bayyana cewa, matukar 'yan Najeriya suka Bola Ahmad Tinubu a zaben 2023, to tabbas kakarsu ta yanke saka, Punch ta ruwaito.

Makinde ya bayyana wannar magana ta goyon baya ne a wani taron gangamin tallata APC da Tinubu da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya Gamu Da Koma Baya A Yayin Da Manyan Yan APC 400 Suka Koma Bangaren Atiku

Masoya Tinubu sun yi tattaki tsakanin kananan hukumomi biyu na Ondo ta Gabas da ta Yamma don nuna kaunarsu ga dan takarar na APC.

Ku zabi Tinubu, ba zai ba ku kunya ba, shawarin dan majalisa ga 'yan Najeriya
2023: Tinubu Ba Zai Ba ’Yan Najeriya Kunya Ba, Dan Majalisa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ku zabi Tinubu, Makinde ya fadi dalilai

A jawabin, Makinde ya bukaci 'yan Najeriya da suk zabi Tinubu a 2023 da ma sauran 'yan jam'iyyar domin ganin ci gaba bayan zaben 2023.

A kalamansa:

"Mun zo ne don yabawa jama'a bisa nuna goyon bayansu ya zuwa yanzu kuma muna tabbatar muku cewa ba za mu baku kunya ba idan kuka zabi dan takararmu na shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu a zaben Fabrairun badi. Asiwaju ba zai ba 'yan Najeriya kunya ba idan aka zabe shi.
"Kun san ni a matsayin danku, kuma ba zan yi fiye da abin da nayi a wa'adina na farko ba da baku zabe ni na wakilce ku a majalisar kasa ba.

Kara karanta wannan

Tinubu: Buhari ya jefa Najeriya a yunwa, amma ya yi wani abu 1 da ya kamat kowa ya sani

"Ina kira gareku da ku zabi dukkan 'yan takarar jam'iyyarmu, APC, a babban zaben 2023 daga kan shugaban kasa har mamban majalisar dokoki na jiha."

A nasa jawabin, dan takarar sanata na Ondo ta tsakiya, Mr Niyi Adegbomire shi ma ya bukaci jama'a da su ba da kuri'unsu ga Tinubu a zaben 2023.

Ya kuma bayyana cewa, Tinubu na da tarihi mai kyau na aiki tukuru a jihar Legas yayin da ya yi gwamna tsawon shekaru takwas.

A jiya ne Tinubu yace tabbas akwai yiwuwar Buhari ya jefa Najeriya cikin yunwa, amma ya tabbatar da daura kasar nan a kan turba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel