2023: Najeriya Zata Amfana da Ziyarar Da Atiku Ya Tafi Kasashen Waje, Kwamitin Kamfe

2023: Najeriya Zata Amfana da Ziyarar Da Atiku Ya Tafi Kasashen Waje, Kwamitin Kamfe

  • Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP yace ziyarar da Atiku ya kai Amurka zata amfanar da 'yan Najeriya nan gaba
  • A wata sanarwa da Kola Ologbondiyan, yace lamarin zai jawo masu zuba hannun jari da farfaɗo da Masana'antu da sauransu
  • Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, yanzu haka yana Amurka, inda yake ganawa da kwararru a fannoni daban-daban

Kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku/Okowa ya tabbatar wa yan Najeriya cewa ziyarar da ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar ya tafi ƙasashen waje zai haifar da sakamako mai kyau nan gaba.

Kwamitin yace sakamakon wannan tafiya, 'yan Najeriya su sa ran ganin zuba hannun jari mai gwaɓi, farfaɗo da sashin kirkire-kirkire da samar da aiki ga matasa da zaran ya karɓi shahadar kama aiki ranar 29 ga Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

2023: Mutane Sun Fito Yayin da Ɗan Takarar AAC Ya Buɗe Kamfen Neman Gaje Buhari a Kano

Ziyarar Atiku Abubakar a Amurka.
2023: Najeriya Zata Amfana da Ziyarar Da Atiku Ya Tafi Kasashen Waje, Kwamitin Kamfe Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Bugu da ƙari, kwamitin yace ziyarar da yanzu haka Atiku yaje Amurka inda ya gana da cibiyar kasuwancin US da sauransu, zai ƙara gina tubali mai kyau ga farfaɗowar tattalin arziki da zaman lafiya a Najeriya.

Jaridar Vangaurd ta rahoto cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin kwamitin kamfen, Kola Ologbondiyan, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace, "Ziyarar Atiku ta maida hankali ne kan tattaunawa da kwararru da nufin lalubo hanyar warware muhimman kalubalen ƙasa da ya haɗa da tattalin arziki da tsaro, wanda gwamnatin APC ta gurgunta."

"Haka nan Atiku na ci gaba da jan hankalin yan kasuwa na gida da kasashen waje da nufin jawo zuba hannun jari, kafa ƙasuwancin da ayyukan yi a muhimman bangarori kamar noma, masana'antu, mai, ilimi da sauransu."

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru

"Mutane ba su manta rawar da Atiku ya taka a matsayin shugaban kwamitin tattalin arziki ba daga 1999 zuwa 2007 lokacin da aka samu warakar tattalin arziki, rage bashi, da cigaba, muka zama ɗaya daga masu tasowa a duniya."

APC ta lalata kusan komai a Najeriya - Kola Ologbondiyan

Ologbondiyan ya nuna damuwarsa kan yadda duk waɗannan tagomashin da Najeriya ta samu a baya, gwamnatin APC karkashin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta lalata su.

Yace lamarin ya yi muni ta yadda shi kansa ɗan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, ba ya iya kamfe da wani abu ɗaya da gwamnatin Buhari ta cimma nasara.

Leadership ta rahoto ya ci gaba da cewa:

"Wannan ne yasa yan Najeriya a ko ina suke ke ci gaba da gangami a bayan Atiku a yunkurin ceto ƙasar mu da dawo da ingantacciyar iskar numfashi ga mutane daga 29 ga watan Mayu, 2023."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Atiku Ya Shilla Kasar Amurka, An Gano Babban Abinda Ya Fitar da Shi Najeriya

A wani labarin Shugaban PDP Na Kasa Ya Maida Martani, Yace Ba Zai Zauna da Ortom don samun sulhu Ba

Yayin da rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP ya buɗe sabon babi, shugaban jam'iyya na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya sha alwashin ba zai yi wani yunkurin ganawa da gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai ba.

Ayu ya yi fatali da shawarin dattawan PDP na Jemgbah, waɗanda suka nemi shugaban jam'iyyar ya zauna da Ortom domin samun maslaha.

Asali: Legit.ng

Online view pixel