Kwankwaso Ba Zai Taba Janye Wa Kowa Ba, Zai Gwabza a 2023, Kakakin Kamfen NNPP

Kwankwaso Ba Zai Taba Janye Wa Kowa Ba, Zai Gwabza a 2023, Kakakin Kamfen NNPP

  • Kakakin kwamitin yakin neman zaɓe na jam'iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya musanta raɗe-raɗin Kwankwaso ka iya janyewa daga takara
  • Johnson ya caccaki masu yaɗa jita-jitar inda ya bayyana cewa Kwankwaso zai gwabza a zaɓen 25 ga watan Fabrairu, 2023
  • Yace nan da mako mai zuwa idan kamfe ya kankama, yan Najeriya zasu ga ainihin magoya bayan Kwankwaso

Ladipo Johnson, mai magana da yawun kwamitin kamfen shugaban kasa na Rabiu Musa Kwankwaso, yace ɗan takarar ba shi da niyyar janye wa kowa.

Johnson ya yi wannan furucin ne a cikin shirin Sunrise Daily na kafar Talabijin ɗin Channels tv ranar Laraba yayin da ake tsaka da jita-jitar cewa ɗan takarar jam'iyyar NNPP ka iya rushe kamfe ga wani.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan PDP Ya Yi Barazanar Yin Murabus Daga Kujerar Gwamna Kan Sharadi Guda

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso Ba Zai Taba Janye Wa Kowa Ba, Zai Gwabza a 2023, Kakakin Kamfen NNPP Hoto: @channelstv
Asali: Twitter
"Babu wata tattaunawar maja duk da lokaci ya ƙure amma babu wata tattauna wa a ƙasa ta rushe kamfe, yakin zaɓensa ko na NNPP a kowane mataki don haɗe wa da wata jam'iyya ko wani ɗan takara."
"Abinda nake nufi a takaice mun shirya zamu tunkari zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun shekara mai kamawa ta kowane hali. Kamar yadda na faɗa yanzun mun maida hankali kan zaɓe."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sanata Kwankwaso na cikin tseren kuma zamu tunkari zaɓe ta kowace hanya, abinda zan iya gaya muku kenan."

- Ladipo Johnson.

Ya kuma caccaki masu yaɗa cewa tsohon gwamnan Kano zai janye wa wani ɗan takara inda ya kira su da masu yaɗa ƙarya mara tushe.

Shin Kwankwaso zai iya kai labari?

Yayin da aka nemi ya yi karin haske kan hasashen cewa zaɓe mai zuwa tsere ne taakanin mutum uku maimakon hudu wanda hakan ya tsame NNPP, Johnson ya ɗora laifin kan kafafen watsa labarai.

Kara karanta wannan

Wani Bawan Allah Umar, Ya Fara Tattaki da Kafa Zuwa Abuja Domin Nuna Goyon Baya Ga Tinubu

Ya ci gaba da cewa:

"Zan iya faɗa muki dalili, mafi yawan kafafen watsa labarai suna kudancin Najeriya, bana son na ambaci Legas, amma ina gaya wa makusanta na cewa ba zai yuwu ka iya hasashen zaɓe ba tare da sanin abinda ke wakana a arewa ba."
"Mun tafka wannan kuskuren lokuta da dama. A zagayen da muka yi watanni uku da suka gabata, ina tabbatar muku cewa idan abubuwa suka kankama mako mai zuwa, zaku gane goyon bayan da Kwankwaso ke da shi a faɗin ƙasar nan."

A wani labarin kuma Wani Malamin Addinin Kirista Yace ba ruwansa da Muslim-Muslim, dun rintsi shi da mabiyasan Tinubu zasu zaɓa

Wani Malamin Addinin kirista, Rabaran Dr. Sam Ogedengbe, yace babu abinda zai hana shi goyon bayan Tinubu a zaben 2023.

Malamin yace duk da Tinubu Musulmi ne amma ba ya mance wa da su duk lokacin bikin kirsimeti.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan PDP Ya Caccaki Yan Takarar Shugaban Ƙasa Biyu, Yace Ba Zasu Kai Labari Ba a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel