2023: Dalilin Da Yasa Zam Goyi Bayan Bola Tinubu, Babban Malami Ya Magantu

2023: Dalilin Da Yasa Zam Goyi Bayan Bola Tinubu, Babban Malami Ya Magantu

  • Wani Malamin Addinin kirista, Rabaran Dr. Sam Ogedengbe, yace babu abinda zai hana shi goyon bayan Tinubu a zaben 2023
  • Malamin yace duk da Tinubu Musulmi ne amma ba ya mance wa da su duk lokacin bikin kirsimeti
  • Yace duk yadda yanayi zai juya shi da masu goyon bayan Cocinsa ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen dangwala wa APC

Lagos - Babban mai taimaka wa na musamman ga tsohon gwamnan Legas, Babatunde Fashola, Wato Rabaran Dr. Sam Ogedengbe, ya yi karin haske kan dalilin da yasa zai goyi bayan ɗan takarar shugaban kasa a inuwar APC.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Ogedengbe, ya kasance shugaban wata ƙungiyar kiristoci na ƙasa (ACLMF) kuma shi ne babban Malami a Majami'ar general overseer of Overcomers Pentecostal Prayer Ministry.

Kara karanta wannan

"Dalilin Da Yasa Cikin Sauki Tinubu Zai Lallasa Atiku, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasan 2023"

Bola Ahmed Tinubu.
2023: Dalilin Da Yasa Zam Goyi Bayan Bola Tinubu, Babban Malami Ya Magantu Hoto: thenation
Asali: Twitter

Malamin Kiristan yace shi da marigayi Dakta Lanre Obembe sun kasance Fastocin Asiwaju Bola Tinubu tun shekarar 1999, kamae yadda PM News ta ruwaito.

Bugu da ƙari, ya ƙara da cewa ya naɗa shi ɗaya daga cikin Fastoci lokacin da ya gina Christian Chapel a Legas House dake Marina tare da Fasto Enoch Adeboye da wasu Malaman Kirista.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa Ogedengbe yace:

"Duk da ɗan takarar APC Musulmi ne amma tsawon shekara 15 da suka gabata bai taɓa gajiya wa wajen kawo mun kyautar Kirsimeti ba da wasu jagororin Kiristoci a Legas da sassan ƙasar nan."
"Hakanan mai ɗakinsa, Sanata Olurami Tinubu ta kasance yar uwa mai kirki kuma mai goyon bayan majami'armu."

Daga ƙarshe, Malamin Addinin Kirista, Ogedengbe, yace duk rintsi duk wuya shi da magoya bayansa ba zasu taɓa watsi da Bola Tinubu ba, inda ya jaddada cewa, "Zamu kaɗa masa kuri'un mu."

Kara karanta wannan

2023: Wani Gwamna Ya Jagoranci Dubbanin Mutane Wurin Tattakin Nuna Goyon Baya Ga Tinubu

A wani labarin na daban Tinubu Ya Bayyana Sunan Da Babban Malamin Addinin Kirista Ya Nada Masa, Tare Da Ma'anar Sunan

Jagoran jam'iyyar jam'iyyar All Progressives Congress, APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce Fasto Enoch Adeboye ya nada masa suna Ibrahim (Abraham).

Tinubu, wanda kuma shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya ce shugaban na RCCG ya nada masa sunan ne lokacin da aka rantsar da matarsa, Remi Tinubu, matsayin fasto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel