Ana Zargin Dan Gwamna Ganduje, Abba, Da Laifin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati

Ana Zargin Dan Gwamna Ganduje, Abba, Da Laifin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati

  • Ana zargin gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, da karkatar da dukiyar gwamnati don amfanin dansa
  • Abba Ganduje na neman kujeran majalisar wakilai na APC mai wakiltar mazabar Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa
  • An ga motoci kimanin 30 dauke da hotunan Abba Ganduje a cikin jami'ar Maitama Sule dake jihar

Kano - Jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) na zargin Abba Ganduje, dan gidan gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje da karkatar da wasu dukiyoyin jihar.

NNPP ta bukaci hukumomi su gaggauta bincikensa.

Abba Ganduje ne dan takarar kujeran majalisar wakilai na APC na mazabar Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa.

Shugaban jam'iyyar ta NNPP, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar, rahoton SR.

Abbah
Ana Zargin Dan Gwamna Ganduje, Abba, Da Laifin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati Hoto: Abubakar Ibrahim
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Bidiyo: Bayan shafe kwanaki a Faransa, dan takarar PDP Atiku ya dawo Najeriya

Doguwa yace jam'iyyarsa ta gano yadda gwamnatin jihar ta karkatar da motocin hukumar amsan harajin jihar KIRS guda 30 wajen yakin neman zaben Abba.

A cewar jawabin:

"Motocin na dauke da hotunan Abba Ganduje kuma ana shirin rabawa shugabannin gunduma na APC a Rimin Gado, Dawakin Tofa da Tofa domin fito-na-fio da Tijjani Abdulkadir Jobe wanda ya raba motoci 20 ga jigogin jam'iyyarsa."

Jawabin ya kara da cewa yanzu haka motocin na ajiye a cikin jami'ar Maitama Sule yayinda ake shirin rabasu.

Yace:

"Muna kira ga hukumar EFCC, ICPC da INEC su gudanar da binciken sace dukiyar gwamnati da kuma saba dokokin zabe."

Ba gaskiya bane, KIRS

Hukumar KIRS ta tayi watsi da zargin kuma ta lashi takobin shigar da shugaban NNPP na Jihar Kano kotu bisa kazafin da yake mata, riwayar Aminiya.

Mai magana da yawun hukumar KIRS, Rabi’u Saleh Rimingado ya fitar ta ce motoci 30 da aka gani like da hotunan Abba Ganduje, dan takarar ya tanade su da kansa.

Kara karanta wannan

APC tayi waje da Minista, Tsohon Gwamna, da Wasu Daga kwamitin zaben Tinubu

Zuwa lokacin hada wannan labari dai ba a samu ji ta bankin Abba Ganduje ba.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel