Jam'iyyar APC Ta Saki Sabon Jerin Sunayen Tawagar Kamfen Shugaban Kasa 2023

Jam'iyyar APC Ta Saki Sabon Jerin Sunayen Tawagar Kamfen Shugaban Kasa 2023

  • Jam'iyyar APC mai mulki fa fitar da sunayen mambobin tawagar yakin neman zaɓen 2023 na karshe
  • Manyan kusoshin jam'iyyar da suka haɗa da gwamnoni sun nuna rashin amince wa da tawagar farko, lamarin da ya jawo tsaiko a APC
  • A Sabon daftarin mambobin, Shugaban APC na kasa da Bola Tinubu sun samu sauyin matsayi, Buhari na nan a matsayin shugaba

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ƙasa ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na mambobin kwamitin yaƙin neman zaben shugaban ƙasa gabanin babban zaɓen 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A baya dai, Sakataren kwamitin kamfen, James Falake, ya saki sunayen mambobi 422 karkashin jagorancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari amma wasu masu ruwa da tsaki suka yi watsi da tawagar.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa Ya Dakatar Yakin Neman Zabe Kan Abu Ɗaya Da Ya Shafi Yan Najeriya

Jam'iyyar APC.
Jam'iyyar APC Ta Saki Sabon Jerin Sunayen Tawagar Kamfen Shugaban Kasa 2023 Hoto: OfficialAPCNigeria
Asali: Twitter

Wannan ci gaban dai ya haddasa Darakta Janar na tawagar kamfen, gwamna Simon Lalong na jihar Filato, ya sanar da cewa za'a sake fitar da sunayen karshe domin shawo kan korafin wasu.

Wane canji sabon jerin sunayen ya kunsa?

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a sabon kwamitin kamfen mai ɗauke da sa hannun Sakataren APC na ƙasa, Iyiola Omisore, saɓanin na farko da Tinubu ya sa hannu, shugaba Buhari ya rike matsayinsa na shugaban kwamitin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma sabanin na farko, shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi sauyin matsayi da Tinubu. Adamu ya koma mataimakin shugaba na I, Tinubu kuma koma mataimaki na II.

Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, na nan a matsayinsa na karamin mataimakin shugabam tawagar kamfe.

Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya rike matsayinsa na Darakta Janar, Kwamaret Adams Oshiomhole a matsayin mataimakin DG, da kuma James Faleke a matsayin Sakatare.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Peter Obi Ya Gana da Wani Gwamnan Arewa, Ya Aike da Muhimmin Sako Ga Tinubu, Atiku da Kwankwaso

Sai dai a halin yanzu, da yawan jiga-jigan APC sun shiga kwamitin kamfen domin rarrshin mambobin da suka nuna fushi kan rashin sanya sunayen mutanen da suka aika.

A wani labarin kuma Abokin Atiku Ya Yi Watsi Da Shi, Ya Faɗi Ɗan Takarar Da Yake So Ya Gaji Buhari a 2023

Jigon jam'iyyar PDP mai adawa a kasar nan, Dr Sampson Orji, ya bayyana cewa Peter Obi ne zabinsa a babban zaben 2023.

Orji, wanda ya nemi tikitin takarar gwamnan Abiya a inuwar PDP, yace Atiku abokinsa ne amma Obi ya fi shi cancanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel