2023: Bidiyon Yadda Atiku da Tinubu Suka Haɗu a Filin Jirgin Sama a Kaduna

2023: Bidiyon Yadda Atiku da Tinubu Suka Haɗu a Filin Jirgin Sama a Kaduna

  • Manyan yan takarar shugaban ƙasa biyu dake sahun gaba, Bola Tinubu da Atiku Abubakar sun haɗu a filin jirgin sama a Abuja
  • Bayanai sun nuna cewa jiga-jigan siyasar biyu sun gaisa da juna yayin da yan tawagarsu ke kiran sunan iyayen gidansu
  • Yayin ganawarsa da manyan arewa, Tinubu ya bukaci Atiku ya janye daga takara ya dawo bayansa kamar yadda ya masa a 2007

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyarAPC, Bola Tinubu, da abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, sun haɗu a sashin manya VIP na Filin jirgin sama watau Azikiwe International Airport dake Abuja.

Jaridar Daily Trust tace duk da ana kakar yaƙin neman zaɓe, kuma duk da bambanci siyasa dake tsakaninsu, yan takarar biyu sun gaisa tare da musayar kalamai.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Tinubu Ya Nemi Atiku Ya Janye Daga Takara, Ya Goya Masa Baya a 2023

Bola Tinubu da Atiku.
2023: Bidiyon Yadda Atiku da Tinubu Suka Haɗu a Filin Jirgin Sama a Kaduna Hoto: pmnews
Asali: UGC

A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta, bayan manyan 'yan takarar biyu sun gaisa da juna an ga nutane dake tare da su na yabon juna suna kiran sunayen yan takararsu.

Duba Bidyon Nan

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ana ganin dai fafatawa zata fi zafi tsakanin 'yan takarar biyu, na jam'iyya mai mulki da kuma na babbar jam'iyyar adawa, a babban zaben 2023.

Bola Tinubu ya gana da kwamitin gamayyar ƙungiyoyin manyan arewa a Kaduna, inda ya nemi Atiku ya saka masa karamcin da ya masa a 2007.

Tsohon gwamnan Legas ɗin yace a zaɓen 2007, ya janye daga takarar shugaban ƙasa kuma ya mara wa Atiku Abubakar baya, bisa haka shi ya janye masa a yanzu.

Atiku ya gudanar da gangami a Kaduna

A wurin gangamin yakin neman zaɓensa da ya gudana yau a Kaduna, Atiku ya sha alwashin magance matsalolin da suka zama karfen ƙafa ga jama'ar jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Baba-Ahmed Ya Gargadi Yan Najeriya Akan Su Guje Wa Yan Takara Masu Nuna Kabilanci da Addini a Zaben 2023

Tsohon mataimakin shugaban ƙasan yace zai kawo karshen ayyukan yan bindiga kuma zai farfaɗo da Masana'antun Kaduna idan har ya ci zaɓen 2023.

A wani labarin kuma Sabuwar Matsala a PDP, Karin Gwamnoni Huɗu Sun Yi Barazanar Juya Wa Atiku Baya Kan Abu Ɗaya

Rikicin jam'iyyar PDP ya sake ɗaukar sabon babi yayin da wasu gwamnoni hudu suka haɗa kai don yakar Wike da makusantansa.

Gwamnonin sun yi barazanar janye wa daga kamfen Atiku idan har ya rasa mafita kuma ya sa Ayu ya yi murabus.

Asali: Legit.ng

Online view pixel