Wata Sabuwa: An Yiwa Ministan Buhari Wankin Babban Bargo Kan Kin Ayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu

Wata Sabuwa: An Yiwa Ministan Buhari Wankin Babban Bargo Kan Kin Ayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu

  • Mataimakin sakataren labaran jam’iyyar APC na kasa, Murtala Ajaka, ya caccaki ministan kwadago, Chris Ngige kan jawabinsa game da Tinubu
  • Ngige dai yaki bayyana dan takarar shugaban kasa da yake goyon baya tsakanin Tinubu da Peter Obi na Labour Party
  • Ajaka ya ce idan har ministan ba zai iya goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa bat oh ya kamata yayi murabus daga kujerarsa

Murtala Ajaka, mataimakin sakataren labaran jam’iyyar APC na kasa, ya yiwa ministan kwadago, Chris Ngige wankin babban barko kan furucin da yayi game da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A wata hira da aka yi dashi a gidan talbijin, Ngige yaki amsa wata tambaya da aka masa inda aka nemi sanin shin zai lamuncewa Tinubu ko kuma Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party zai marawa baya.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

Ngige da Tinubu
Wata Sabuwa: An Yiwa Ministan Buhari Wankin Babban Bargo Kan Kin Ayyana Goyon Bayansa Ga Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Ministan kwadagon ya bayyana tambayar a matsayin mai matukar wahala, inda yace su dukka biyun abokansa ne kuma zai bayyana zabinsa a gaban akwatin zabe.

An bukaci Ngige yayi murabus idan har ba zai yi Tinubu ba

Ajaka yace lallai dole Ngige yayi murabus idan har ba zai iya marawa dan takarar shugaban kasa na APC, Tinubu baya ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, 8 ga watan Oktoba, Ajaka yace an dade da kammala zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na APC, kuma jam’iyyar ta fitar da Tinubu, jaridar TheCable ta rahoto.

Ya ce ya kamata shugabannin jam’iyyar su ajiye kudurorinsu a bayansu don kawowa jam’iyyar kujerar shugaban kasa a 2023.

Ya ce:

“Ana sanya ran minista mai ci a gwamnatin APC ya zama mai aminta da shugabancin Bola Ahmed Tinubu a 2023, wanda shi da sauran shugabannin jam’iyya suka sha aiki don tabbatar da nasarar wannan gwamnati a 2015 wanda a cikinta suke aiki a yanzu.

Kara karanta wannan

Majiya Ta Bayyana Ranar Dawowar Tinubu Najeriya, Zai Halarci Wani Muhimmin Taro A Abuja

“Bai kamata Cif Ngige da sauran masu mukamai a APC, musamman majalisar tarayya su manta da sauri cewa suna rike da mukaman jam’iyya ne, don haka ya kamata su kare shi da duk abun da yake bukata, amma idan ba za su kare ra’ayin APC ba a idon duniya da na dan takarar shugaban kasarmu (Tinubu), ina ganin zai fi kyautuwa su janye daga gwamnatin da APC ta kafa.”

Vanguard ta rahoto cewa mataimakin kakakin na APC yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya saita yan majalisarsa sannan ya tabbatar da jajircewarsu wajen kawowa APC mulki a 2023.

Ya dasa ayar tambaya kan dalilin da zai sa Ngige, ministan jam’iyya mai mulki mai ci, ba zai iya ayyana zabinsa na dan takarar shugaban kasa a gidan talbijin na kasa ba.

Ministan Buhari Ya Shiga Rudani, Ya Fadi Sunayen 'Yan Takarar Shugaban Kasa Biyu da Yake Son Zaben Daya a 2023

Kara karanta wannan

2023: Mata a yankin su Peter Obi sun yi biris dashi, sun yi gangamin nuna kaunar Tinubu

A baya mun ji cewa ministan kwadago da daukar ma’aikata, Chris Ngige, yace ba zai bayyana dan takarar shugaban kasa da yafi so ba a zaben 2023.

Ngige ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da ya bayyana a shirin ‘Politics Today’ na gidan talbijin din Channels.

Da aka tamabaye shi game da wanda zai marawa baya tsakanin Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyarsa, da Peter Obi na Labour Party, Ngige ya bayyana tambayar a matsayin mai wahala.

Asali: Legit.ng

Online view pixel