2023: Bola Tinubu Ya Dakko Gwamna Buni Na Yobe, Ya Nada Shi a Wani Mukamin Kamfe

2023: Bola Tinubu Ya Dakko Gwamna Buni Na Yobe, Ya Nada Shi a Wani Mukamin Kamfe

  • Bola Tinubu, mai neman zama shugaban kasa a inuwar APC na ci gaba da naɗa mambobin tawagar yaƙin neman zaɓe
  • Tsohon gwamnan Legas ya ɗakko gwamna Mala Buni na jihar Yobe, ya naɗa shi a wani muhimmmin muƙami na kusa-kusa
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan INEC ta halasta wa jam'iyyu fara kamfe don tunkarar zaɓen 2023

Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, a wata kujerar tawagar kamfe.

Jaridar Vanguard tace Tinubu ya naɗa gwamna Buni a matsayin mashawarci na musamman kan harkokin, "Haɗin kai da ƙara dunƙulewar jam'iyya," na tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu/Shettima a 2023.

Kara karanta wannan

2023: Mun Gano Kuskuren Da Muka Tafka, Atiku Ya Magantu Kan Rikicin PDP da Su Gwamna Wike

Mai Mala Buni na jihar Yobe.
2023: Bola Tinubu Ya Dakko Gwamna Buni Na Yobe, Ya Nada Shi a Wani Mukamin Kamfe Hoto: Vangaurdngr.com
Asali: UGC

Leadership tace A wata wasiƙa da aka tura ga Gwamna Buni kuma mai ɗauke da sa hannun Bola Tinubu, mai neman zama shugaban ƙasan yace, "Naɗin da ya dace kuma a lokacin da ya kamata."

A cewar tsohon gwamnan Legas, bisa la'akari da nasarorin da Buni ya cimma a siyasance da kyakkyawan shugabanci abin misali da kwatance da yake aiwatarwa a matsayin gwamnan Yobe, muƙamin ya je inda ya dace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun ji daɗi da ka shigo tawagar kamfe ɗinmu. Mun san zaka yi bakin gwarwado a wannan nauyi da aka ɗora maka domin mu gudanar da Kamfe mai tsafta da zai kai mu ga nasara a 2023."
"A tare, ba wai mu kaɗai ba zamu tabbatar da nasara a babban zaɓen dake tafe a watan Fabrairu, 2023 amma yana da kyau mu tafiyar da Najeriya zuwa ɗaukaka ta hanyar ɗora wa daga inda APC da shugaba Buhari suka tsaya a fannin ci gaba."

Kara karanta wannan

2023: Jigon PDP a Kano Ya Tono Asalin Rikici, Yace Babu Hujjar Da Ta Nuna Atiku Ya Yi Wa Wike Alkawari

- Bola Ahmed Tinubu.

APC ta samu ƙarin goyon baya a Edo

A wani labarin kuma Atiku Da PDP Sun Yi Rashin Wani Babban Jigo da Ɗaruruwan Mambobi, Sun Koma APC a Jihar Edo

Jigon jam'iyyar PDP a yankin ƙaramar Hukumar Ovia ta kudu-yamma, jihar Edo da ɗaruruwan mambobi sun koma APC.

Hon. George Edokpolor, yace babu wani mutumi mai cikakken hankali a mazaɓar Ovia da zai ci gaba da zama a jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel