Babu Inda Atiku Ya Yi Alkawarin Daukar Wike a Matsayin Mataimaki, Jigon PDP

Babu Inda Atiku Ya Yi Alkawarin Daukar Wike a Matsayin Mataimaki, Jigon PDP

  • Muazu Magaji, jigon PDP a jihar Kano yace babu wata hujja da ta nuna Atiku ya yi wa gwamna Wike alƙawarin mataimaki
  • Wani kwamiti da PDP ta kafa ya shawarci baiwa Wike matsayin amma Atiku ya nuna ya fi natsuwa da gwamna Okowa
  • Saɓani ya shiga tsakanin Atiku da gwamnan Ribas tun bayan kammala zaɓen fidda gwani a watan Mayu

Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Kano a inuwar PDP, Mu'azu Magaji, yace mai neman zama shugaban kasa, Atiku Abubakar, bai yi alƙawarin ɗaukar gwamna Wike na Ribas a matsayin abokin takara ba.

Mu'azu Magaji, wanda ake wa laƙabi da Dan Sarauniya ya jaddada cewa babu wata kwakkwarar shaida da ta nuna ɗan takarar PDP ya ɗauki wannan alƙawarin.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu, Obi Ko Kwankwaso? Namadi Sambo Ya Faɗi Wanda Ya Dace Ya Gaji Buhari a 2023

Gwamna Wike da Atiku Abubakar.
Babu Inda Atiku Ya Yi Alkawarin Daukar Wike a Matsayin Mataimaki, Jigon PDP Hoto: @Channelstv
Asali: Twitter

Magaji ya yi wannan furucin ne ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, 2022 yayin hira da Channels TV cikin shirin Sunrise Daily.

Ɗan sarauniya yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ina mai jaddada cewa ba bu wata ƙwaƙƙwarar Hujja da ta nuna cewa Atiku ya yi alƙawarin zaɓar gwamna Wike a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa."
"Akwai bukatar mu fahimci cewa abun ba kadarar kai da kai bace, a koda yaushe ina kokarin jan hankalin mutane kan haka. Babu wata hanya kuma ba wata shaida."
"Babu ko mutum ɗaya da zai iya cewa mun zauna da ɗan takarar shugaban ƙasa a sirrince kuma yace zan ba ka matsayin ɗan takarar mataimaki. Zaɓen abokin takara wata alfarma ce kuma sai an bi matakai."

Yadda saɓanin Atiku da Wike ya samo asali

Gwamna Wike da Atiku Abubakar sun raba gari ne tun bayan ayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasa a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin PDP a watan Mayu.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito Yayin da Ake Jita-Jitar Wani Gwamnan PDP Ya Jingine Atiku, Ya Goyi Bayan Obi a 2023

Wani rahoto ya yi ikirarin cewa kwamitin da PDP ta kafa ya gabatar da Wike a matsayin abokin takara amma Atiku ya nuna ya fi nutsuwa da gwamna Okowa na jihar Delta, lamarin da ya ƙara harzuƙa Wike.

Wike da mutanensa ciki har da gwamnoni masu ci da tsofaffi sun jaddada buƙatar cewa Iyorchia Ayu ya yi murabus daga shugaban PDP na ƙasa domin miƙa kujerar ga ɗan kudu.

Sun ce ba zai yuwu arewa ta haɗa tikitin shugaban ƙasa da muƙamin shugaban jam'iyya ba, sun kuma yi ikirarin cewa Ayu ya ɗauki alƙawarin yin murabus idan har ɗan arewa ya lashe tikitin PDP.

Sai dai saɓanin ikirarin tsagin Wike, Ayu ya jaddada cewa dole a bari ya kammala wa'adinsa na shekaru hudu.

A wani labarin kuma Gwamnan Eikiti na jam'iyyar APC Ya Rushe Majalisar Kwamishinoni da Naɗe-Naɗen Gwamnatinsa

Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti ya sanar da rushe baki ɗaya majalisar zartarwan gwamnatinsa ranar Laraba.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan, Wike da Wasu Kusoshin PDP Ba Su Halarci Taron Kaddamar da Litattafai da Kamfen Atiku Ba

Wannan matakin na zuwa ne yayin da ake shirin rantsar da sabon zaɓaɓɓen gwamna mai jiran gado, Biodun Oyebanji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel