'Dalilin Da Yasa Wajibi 'Yan Arewa Su Zabo Bola Ahmed Tinubu a 2023'

'Dalilin Da Yasa Wajibi 'Yan Arewa Su Zabo Bola Ahmed Tinubu a 2023'

  • Mai neman zama Sanatan Kaduna ta tsakiya, Muhammad Dattijo, yace 'yan Arewa ba su da zabin da ya wuce Tinubu/Shettima a 2023
  • Da yake tsokaci kan irin wanda da ya dace ya gaji Buhari, Dattijo yace yan arewa na bukatar mutumin dake ƙaunar yankinsu
  • Dattijo ya yi ikirarin cewa Tinubu da abokin takararsa ne suka haɗa duk wani abu da ake bukata duba da jihohin da suka mulka

Kaduna - Ɗan takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya karkashin inuwar APC, Muhammad Sani Dattijo, ya yi bayanin dalilin da yasa yake ganin ya dace 'yan arewa su zaɓi Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima.

A cewarsa, mai neman shugaban ƙasa a APC, Bola Tinubu, da abokin takararsa, Sanata Kashim Shettima, su ne suka cancanta su gaji shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari kuma su ɗora daga inda ya tsaya.

Kara karanta wannan

2023: Nasihar da Shugaba Buhari Ya Yi Wa Yan Takarar Shugaban Kasa 18 a Wurin Taron Abuja

Shettima tare da Bola Tinubu.
'Dalilin Da Yasa Wajibi 'Yan Arewa Su Zabo Bola Ahmed Tinubu a 2023' Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Daily Trust tace Dattijo ya yi wannan furucin ne yayin kaddamar da matasa 2,000 daga sassan kananan hukumomi 23 dake jihar Kaduna, waɗanda zasu yi aiki don kai APC ga nasara karkashin Tinubu Shettima Support Group.

Dattijo ya roki matasan su shiga lungu da saƙo na yankunansu su fahimtar da masu kaɗa kuri'a abinda yasa ya rataya a wuyansu zaɓi jam'iyyar APC da dukkan 'yan takararta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ruwayar Vanguard, Ɗan takarar Sanatan yace, "Ya kamata 'yan arewa su tabbata jam'iyyar APC ta lashe zaɓe mai zuwa saboda ita kaɗaice jam'iyyar da ta sanya su a zuciyarta idan aka kwatanta da saura."

"Wannan ne dalilin da yasa matasa ya rataya a wuyan mu, mu zaɓi mutanen da suka dace domin haskaka gobenmu. Muna buƙatar wanda ke kaunar yankinmu da ƙasar mu baki ɗaya."

Kara karanta wannan

2023: Na Sadaukar da Rayuwata da Komai Ga Al'ummar Jihar Katsina, Ɗan Takarar APC Dikko

"Tinubu da Shettima, sune waɗanda ya dace mu dangawala wa kuri'un mu a zaɓe mai zuwa saboda la'akari da kyakyawan shugabancin da suka gudanar lokacin suna gwamna a jihohinsu."

Babachir Lawan ba shi da tasiri a yankinsa - Oshiomhole

A wani labarin kuma Tsohon shugaban APC ya caccaki Babchir Lawan da Yakubo Dogara kan shirinsu na juya wa Tinubu baya

Kwamaret Adams Oshiomhole yace tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, ba shi da tasiri ko a yankinsa.

Da yake tsokaci kan banɗarewar Dogara da Lawal, Tsohon shugaban APC yace ba zasu rasa bacci ba kan waɗannan mutanen biyu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel