Gwamna Tambuwal Ya Maye Gurbin Gwamna Fayemi a Matsayin Shugaban Kungiyar Gwamoni

Gwamna Tambuwal Ya Maye Gurbin Gwamna Fayemi a Matsayin Shugaban Kungiyar Gwamoni

  • A yau ne muke samun labarin yadda aka nada gwamnan jihar Sokoto a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya
  • Aminu Tambuwal ne shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar adawa ta PDP kuma yanzu ya zama shugaban gwamnonin Najeriya
  • Har yanzu ana ci gaba da kai ruwa rana kan mukaman cinkin gida a jam'iyyar PDP, lamarin da ke kara jefa jam'iyyar cikin rudani

FCT, Abuja - Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya maye gurbin takwaransa na jihar Ekiti, Kayode Fayemi a shugabancin kungiyar gwamnonin Najeriya, Punch ta ruwaito.

Tambuwal ya karbi shugabancin ne a yau Alhamis 22 ga watan Satumba a taron majalisar tattalin arzikin kasa da aka yi a Aso Rock Villa, Abuja, inda Fayemi ya mika masa sandar mukamin.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan Lantarki Sun Yi Barazanar Kashe Wutan Najeriya Gaba Daya

Gwamna Tambuwal ya zama sabon shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya
Gwamna Tambuwal Ya Maye Gurbin Gwamna Fayemi a Matsayin Shugaban Kungiyar Gwamoni | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Sanarwar da daraktan yada labarai na NGF, Abdulrazaque Bello Barkindo ya fitar ta ce:

"Tambuwal ya yi aiki tukuru cikin gaskiya da aminci a lokacin da yake mataimakin shugaban kungiyar karkashin shugabancin Dr Fayemi na shekaru hudu."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hakazalika, sanarwar ta ce, Tambuwal zai rike mukamin ne har zuwa watan Mayun 2023, lokacin da za a sake gudanar da zabe sahihi na kungiyar, rahoton Vanguard.

Majiya ta ruwaito cewa, a kwanan nan ne aka zabi Fayemi a matsayin shugaban kungiyar gwamnatocin shiyya da kasashe a Saidia ta jihar Casablanca a kasar Morrocco.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya taya Tambuwal murna, ya kuma yiwa gwamna Fayemi addu'ar nasara a ayyukansa na kasa Najeriya da ma wanda ya samu a kasar waje.

Sanarwar ta kuma, Aminu Tambuwal zai fara aiki ne a ofishin shugabancin gwamnonin a ranar 16 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP Sun Tsoma Baki a Rikicin Atiku da Wike, Sun Faɗi Kullin da Suke Gabanin 2023

Kwamishinan Tsaro na Gwamna Tambuwal ya Koma APC a Sokoto

A wani labarin na daban kuma. al'amuran siyasa a jihar Sokoto na kara canzawa gabanin babban zaben badi. Jam’iyyar PDP mai mulkin jihar ta rasa wasu ‘ya’yanta zuwa jam’iyya mai mulkin kasa; APC.

Kanar Garba Moyi (rtd), wanda shi ne kwamishinan ayyuka da harkokin tsaro a gwamnatin Gwamna Aminu Tambuwal ya fice daga PDP ya tsunduma APC, The Nation ta ruwaito.

Ficewar Moyi na zuwa ne jim kadan bayan jam’iyyar ta karbi Kalanjeni da kansilolinsa wadanda su ma suka fice daga PDP zuwa APC a karkashin Sanata Aliyu Wamakko a jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel