Bola Tinubu Ya Dira Gidan Tsohon Shuhaban Kasa Obasanjo, Sun Sa Labule

Bola Tinubu Ya Dira Gidan Tsohon Shuhaban Kasa Obasanjo, Sun Sa Labule

  • Jagoran APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya isa gidan tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, jihar Ogun
  • Bayanai sun nuna cewa da zuwansa, kai tsaye ya shiga ganawar sirri da Obasanjo game da batun takararsa a 2023
  • Tun kafin zuwansa, masoya da magoya bayan ɗan takarar shugaban kasan suka yi dafifi ba masaka tsinke a gidan

Ogun - Ɗan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya dira gidan tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da ke Abeokuta, jihar Ogun.

Daily Trust ta ce, Tinubu tare da rakiyar yan tawagarsa, ya shiga ganawa da Obasanjo a wani ɓangaren cigaba da ziyarar neman shawari da bin matakan cimma burinsa na zama shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Dira Jihar Ogun, Zai Sa Labule da Tsohon Shugaban Ƙasa Kan Muhimmin Abu

Bola Tinubu.
Bola Tinubu Ya Dira Gidan Tsohon Shuhaban Kasa Obasanjo, Sun Sa Labule Hoto: Abubakar Kurbe/facebook
Asali: Facebook

Jirgin Tinubu ya dira da misalin ƙarfe 1:00 na rana a harabar katafaren gidan Obasanjo (OOPL), Oke Mosan, Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Tsohon gwamnan ya samu tarba daga gwamna Dapo Abiodun na Ogun, mataimakinsa, Noimot Salako-Oyedele, tsoffin gwamnoni, Olusegun Osoba, Gbenga Daniel, da jiga-jigan APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jim kaɗan bayan isarsa, Bola Tinubu, ya tafi kai tsaye suka fara tattaunawa cikin sirri da tsohon shugaban a gidan Obasanjo da ke harabar Laburarin OOPL.

Daga cikin yan tawagar da suka yi wa Tinubu rakiya har da kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, Chief Bisi Akande, Nuhu Ribadu da sauran su.

Masoya sun yi dafifi a gidan Obasanjo

Legit.ng Hausa ta gano cewa tun da farko, magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasan sun yi cincirindo a gidan Obasanjo, suka maida wurin tamkar filin kamfe.

Kara karanta wannan

Zan Yanke Hukunci Kan Ko Zan Fice Daga Jam'iyyar Kwankwaso A Wannan Makon, Shekarau Ya Magantu

Wannan shi ne karo na uku da Jagoran APC na ƙasa ya ziyarci jihar Ogun kan burinsa na zama shugaban ƙasa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

A watan Fabrairu ya gana da baki ɗaya Sarakunan jihar, yayin da ranar 4 ga watan Yuni, ana gab da zaɓen fidda gwani, ya gana da Deleget ɗin Ogun a Abeokuta, inda ya faɗi rawar da ya taka a nasarar Buhari 2015.

A wani labarin kuma Tsohon makusancin Buhari ya yi hasashen cewa Kwankwaso ne zai lashe zaɓen 2023 bisa wasu dalilai

Buba Galadima, babban jigon jam'iyya mai kayan marmari ya yi hasashen Kwankwaso zai lashe zaɓen shugaban kasa a 2023.

Tsohon makusancin shugaba Buhari ya bayyana yadda tsohon gwamnan Kano zai yi nasara a jihohin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel