Shekarau Zai Fita Daga NNPP Ta Kwankwaso Ya Koma PDP Saboda Wasu Alƙawurra 'Masu Tsoka' Da Atiku Ya Masa

Shekarau Zai Fita Daga NNPP Ta Kwankwaso Ya Koma PDP Saboda Wasu Alƙawurra 'Masu Tsoka' Da Atiku Ya Masa

  • Sanata Ibrahim Shekarau mai wakiltan Kano Central na daf da ficewa daga jam'iyyar NNPP mai kayan marmari zuwa jam'iyyar PDP saboda wasu alkawurra da Atiku Abubakar ya yi masa
  • Wasu majiyoyi da ke da masaniya kan lamarin sun ce Shekarau ya gana da Atiku Abubakar da mataimakinsa Ifeanyi Okowa da Iyorchia Ayu shugaban PDP na kasa sun kammala shirin komawarsa
  • Wasu jiga-jigan jam'iyyar NNPP sun nemi ganin tsohon gwamnan na Jihar Kano don tattaunawa da shi kan batun ficewarsa daga jam'iyyar amma bai yarda ya gana da su ba

Idan ba an samu wani canji ba, tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau zai sanar da ficewarsa daga NNPP zuwa PDP biyo bayan wani alƙawari 'mai tsoka' da aka ce dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar ya masa.

Kara karanta wannan

Bayan Shafe Tsawon Watanni Yana Jinya A Waje: Tsohon Shugaban Najeriya Ya Dawo Kasar

Mista Shekarau, wanda ke wakiltar Kano Central, ya sanar da ficewarsa a hukumance daga APC zuwa NNPP cikin wata wasika da shugaban majalisa, Lawan Ahmad ya karanto a ranar 29 ga watan Yuni.

Ibrahim Shekarau
Shekarau Zai Fita Daga NNPP Ya Koma PDP Saboda Wasu alƙawurra 'Masu Tsoka' Da Atiku Ya Masa. Hoto: @daily_nigerian.
Asali: Facebook

Duk da samun tikitin takarar sanata ba tare da hamayya ba a NNPP, Daily Nigerian ta tattaro cewa Mista Shekarau ya sulala ya tafi Legas a ranar 24 ga watan Yuni don ganawa da ɗan takarar shugaban kasa na Labour Party, Peter Obi don ya masa mataimaki.

An fahimci cewa tattaunawar da ya ke yi da Labour Party ya rushe ne bayan APC da PDP sun fara zawarcin tsohon gwamnan na jihar Kano.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jiga-jigan Jam'iyyar NNPP sun nemi ganin Shekarau amma abin bai yi wu ba

Lokacin da shugabannin NNPP suka gano shirin da Shekarau ke yi na sauya sheka, wata tawaga na mutum 3 da ta kunshi dan takarar gwamna Abba Kabir Yusuf, ɗan takarar sanata na Kano South, Kawu Sumaila da ɗan takarar majalisar wakilai Kabiru Rurum, sun nemi ganawa da shi a daren ranar Juma'a a Abuja, amma Shekarau ya ƙi gana wa da su.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Ya Naɗa Gwamnan Arewa a Matsayin Shugaban Kwamitin da Zai Rarrashi Gwamna Wike

Ƙwararran majiyoyi da suke da masaniya kan matakin da Mista Shekarau ke shirin dauka da kuma tarurruka mabanbanta da ya yi da ɗan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da mataimakinsa Ifeanyi Okowa; da shugaban PDP na kasa Iyorchia Ayu sun ce tsohon gwamnan ya 'cimma matsaya' da PDP kuma ana sa ran zai sanar da sauya shekararsa nan bada dadewa ba.

A cewar majiyar, tsohon gwamnan ya kira taron gaggawa na mashawartansa na siyasa, da ake kira kwamitin Shura, don sanar da su sabon matakin.

Daily Nigerian ta tattaro cewa kwamitin za ta gana a ranar Talata (yau) misalin ƙarfe 4 na yamma don kammala shirin sauya shekar da kuma yadda za su kare matakin na Shekarau saboda yiwuwar suka daga yan siyasa.

Atiku Abubakar zai kawo wa Shekarau ziyara a gidansa na Mundubawa

Majiyar ta kara da cewa a matsayin wani shiri na sauya shekar, ɗan takarar shugaban kasa na PDP Atiku Abubakar zai kawo wa Mista Shekarau ziyara a gidansa na Mundubawa don 'zawarcinsa' kafin ya sanar da ficewarsa a hukumance daga NNPP.

Kara karanta wannan

Ba gaskiya bane: Gwamna dan rashawa da Buhari ya yiwa afuwa ya musanta batun yin takara a 2023

"Maganar gaskiya shine Atiku ya masa wasu alkawurra masu tsoka kamar kujerar minista da guraben aiki a ma'aikatu. Baya ga nada shi matsayin shugaban kamfen na Arewa Maso Yamma wanda zai rika kula da kudaden yakin neman zabe na yankin," in ji majiyar.

Wata majiyar na kusa da Shekarau ta ce sanatan ya yanke shawarar fita daga NNPP ne saboda jam'iyyar bata bawa wasu na kusa da mukamai ba.

"NNPP ta bawa Shekarau kujerar sanata ba tare da bawa abokan siyasarsa komai ba. Don haka akwai makusantarsa suna nuna damuwar cewa ya sama wa kansa tikiti ba tare da kokarin ya sama musu komai ba," in ji majiyar.

Martanin kakakin Shekarau

An yi kokarin ji ta bakin Kakakin Shekarau, Sule Yau Sule, amma ba a same shi ba har zuwa lokacin wallafa wannan rahoton.

Shekarau Ya Fita Daga APC, Ya Koma NNPP Ya Haɗe Da Kwankwaso

Tunda farko, Sanata Ibrahim Shekarau, mai wakiltar Kano ta Tsakiya ya fita daga jam'iyyar APC mai mulki a kasa ya koma NNPP mai kayan marmari, rahoton aminiyya.

Kara karanta wannan

Yarda Zai Yi Wa Tinubu Aiki ya Jefa Gwamna a Matsala, Ana yi wa Addininsa Barazana

Tsohon gwamnan na Kano ya fice ne karkashin jagorancin tsohon gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso, jigo na kasa a jam'iyyar ta NNPP.

Yakubu Yareema, wani na hannun daman Malam Shekarau ya sanar da hakan a yammacin ranar Talata kamar yadda Freedom Radio ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel