Atiku v Wike: Barakar Cikin PDP Ta Yi Zurfi, Jam’iyya Ta Gagara Yin Muhimmin Taro

Atiku v Wike: Barakar Cikin PDP Ta Yi Zurfi, Jam’iyya Ta Gagara Yin Muhimmin Taro

  • Babu jituwa tsakanin Atiku Abubakar da aka tsaida takara a PDP da bangaren Nyesom Wike
  • Gwamna Wike yana kusantar ‘Yan jam’iyyar APC yayin da Jam’iyya ke neman hanyar yin sulhu
  • An fara maganar a sauke Shugaban PDP na kasa, a karshe dai an fasa taron PDP-NEC da aka shirya

Abuja - Halin da ake ciki a jam’iyyar hamayya ta PDP ya kara rincabewa. Punch ta fitar da rahoton nan a ranar Alhamis, 11 ga watan Agusta 2022.

Tun da Atiku Abubakar ya ki daukar Gwamna Nyesom Wike, ya zabi Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa, ake ta samun rashin jituwa a PDP.

Biyo bayan zabin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa, Nyesom Wike yana ta ganawa da gwamnoni da kuma wasu manyan jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Ta karewa PDP a Sokoto yayin da fitaccen kwamishina ya kaura, ya koma APC

Legit.ng Hausa ta rahoto Gwamnonin APC sun yi zama da Wike, bayan haka ya kira wasu jiga-jigan APC domin su kaddamar da ayyukan da ya yi.

A haka ‘Dan siyasar ya hadu da tsohon gwamnan Sokoto, Sanata Aliyu Wammako a Fatakwal, bayan an ga ya gayyato Gwamna Babajide Sanwo Olu.

Kafin nan kuma Gwamna Dave Umahi da Rabiu Musa Kwankwaso sun yi zama da Wike a gida. Sai yanzu aka ji yana nuni ga ficewa daga jam’iyyar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Atiku
Atiku Abubakar Hoto: Atiku.org
Asali: Facebook

Za a tunbuke Shugaban PDP?

An rahoto cewa mutanen Wike sun dage sai an sauuke shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, amma da alama ‘yan majalisar NWC suna tare da Ayu.

Wasu sun fara bada shawarar a canza shugaban jam’iyyar, sai a fake da cewa bai da lafiya. Masu wannan ra’ayi suna ganin ta haka ne za a lallabi Wike.

Kara karanta wannan

Rikicin Atiku da Wike: Jam'iyyar PDP ta dage zaman NEC saboda ta'azzarar rikicin gida

BOT ta gagara dinke baraka

Jam’iyyar PDP ta na kokarin shawo kan sabanin da aka samu, amma har yanzu ‘yan majalisar BOT ba su iya dinke wannan mummunar barakar ba.

The Nation tace an dakatar da taron majalisar koli na NEC wanda jam’iyyar PDP tayi niyyan kira. Daga yau zuwa ranar Juma’a ya kamata ayi zaman.

Rahoton yace rigimar da ta shiga tsakanin bangaren Gwamna Wike da ‘dan takaran shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ne ta jawo aka daga taron.

Sakataren PDP na kasa, Sanata Samuel Anyanwu ya bada sanarwar fasa wannan zama na majalisar NEC, yace za a sa ranar da aka maida zaman.

Nnamani ya yabi Tinubu

An samu rahoto Dr. Chimaroke Nnamani yi Allah-wadai da masu sukar Bola Tinubu, duk da sabaninsu, yace ba a taba yin ‘dan siyasa irin Tinubu ba.

A shafin Twitter, Sanatan Enugu ya bada shawarwari na musamman ga Bola Tinubu da kuma masu kamfe da halin lafiyar ‘dan takaran a zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Ko ba Wike Zan iya nasara a zaben 2023, Atiku ya shaidawa Dattawan PDP

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel