Shugabanci Nagari Kadai Zai Hana Juyin Mulki – Muhammadu Buhari

Shugabanci Nagari Kadai Zai Hana Juyin Mulki – Muhammadu Buhari

  • Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ce Daukaka dimokuradiyya da shugabanci na gari ne kadai maganin juyin mulki a Nahiyar Afrika
  • Buhari ya yabawa shugabankasar Liberia akan kokarin da yayin na shawo kan matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da matasar kasar keyi
  • Shugaban kasar Libria George Weah ya godewa shugaba Buhari kan halarta bikin shekaru 175 da samun ‘yancin kai na kasar Laberiya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Monrovia - Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Talata a birnin Monrovia, kasar Laberiya, ya ce inganta dimokuradiyya da shugabanci na gari ne kadai maganin juyin mulki.

Ya kuma yi kira ga shugabannin kasashen yammacin Afirka da su yi iya kokarinsu wajen gudanar da zabe cikin aminci da gaskiya.

Wannan, ita ce hanya daya tilo da zata magance matsalar hambarar da gwamnati a nahiyar, kamar irin wanda ya faru a kasar Mali a shekara (2021), kasar Guinea a shekara (2021) da Burkina Faso a shakara (2022).

Kara karanta wannan

Jirgin Shugaban Najeriya Buhari ya Dura kasar Laberiya Wajen Bikin ‘Yancin kai

Buhari
Shugabanci Nagari Kadai Zai Hana Juyin Mulki – Muhammadu Buhari FOTO Legit.NG
Asali: Depositphotos

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi a taron bikin cikar kasar shekaru 175 da samun ‘yancin kai na kasar Laberiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan haka Buhari ya yabawa takwaransa na Laberiya, Dokta George Weah, kan kokarin da ya yi na shawo matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da dubban matasan Kasar ke yi.

A nasa bangaren, Weah ya godewa Buhari bisa zuwansa, inda ya ce:

“Na gode shugaban kasa da kuma mutanen Najeriya nagari. Idan ba tare da goyon bayanku ba, da ba mu samu zaman lafiya ba.”

Ka Mutunta Alƙawarin Da Ka Ɗauka, Jigon APC Ya Faɗa Wa Gwamna Wike

A wani labari kuma, Rivers - Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Ribas, Chief Chukwuemeka Eze, ya yi kira ga gwamnan jihar, Nyesom Wike, ya mutunta alƙawarin da ya ɗaukar wa yan Najeriya yayin zaɓen fidda ɗan takarar shugaban kasa na PDP.

Kara karanta wannan

Muhimmacin Ziyarar Shugaba Buhari Kasar Liberia - Garba Shehu

Eze, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya tunatar da Wike alƙwarin da ya ɗauka cewa zai goyi

Asali: Legit.ng

Online view pixel