Matasan yankin Kabilar Ibo sun bayyana goyon bayan su ga Takarar Tinubu da Shettima

Matasan yankin Kabilar Ibo sun bayyana goyon bayan su ga Takarar Tinubu da Shettima

  • Matasan yankin kudu maso gabas sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shettima
  • Matasan kungiyar CSEPY sun ja hankalin Mutane akan cigaban da Tinubu da Shettima suka kawo wa jihohin su a lokacin da suka rike mukamin gwamna
  • Kungiyar CSEPY sun yi kira da ayi watsi da siyasar kabilanci da addini a zabi ‘dan takarar da zai hada kan yan Najeriya

Jihar Imo - Matasan yankin kudu maso gabas sun bayyana goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Sanata Kashim Shetima. Rahoton The Nation

Matasan, a karkashin kungiyar Conferment of South East Progressive Youths (CSEPY), sun ce, suna goyon bayan tikitin Tinubu da Shettima ne saboda yakinin da suke dashi na kawo wa kasar gyarar da take bukata.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu : Kashima Shettima ya kai wa Buhari ziyara a fadar shugaban kasa

Kungiyar ta kuma yi alkawarin marawa jam’iyyar APC a shiyyar baya ta hanyar tabbatar da cewa ‘yan takarar jam’iyyar sun samu nasara a zaben 2023 mai zuwa.

Tinubu
Matasan yankin Kabilar Ibo sun bayyana goyon bayan sa ga Takarar Tinubu da Shettima FOTO THE NATION
Asali: Twitter

Matasan sun ja hankali mutane akan irin cigaban da Tinubu suka kawo wa jihohin su a lokacin dukannin su ya rike mukamin gwamna a jihar sa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wata sanarwa da shugabansu kungiyar Barrista Emeka kalu ya fitar a taron da suka gudanar a Okigwe jihar Imo.

Matasan yankin kudu maso gabas sun bayyana goyon bayansu ga takarar Tinubu da Shettima duk da cewa dan uwan su, Mista Peter Obi ya fito takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour (LP), ya nuna sha'awar su na goyon bayan cancanta bisa sun zuciya.

Emeka ya ce:

“A wannan lokaci na rayuwar mu, ya zama dole ne mu yi watsi da siyasar kabilanci da addini, mu zabi ‘yan takara masu ra’ayin hada kan yan Najeriya.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hotuna sun bayyana, Tinubu ya kaddamar da Shettima a Abuja

Atiku: Banyi Watsi Da Wike Ba, Na zabi Dan Takarar Da Zan Iya Aiki Da Shi ne

A wani labari kuma, Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce bai zabi Nyesom Wike, gwamnan Rivers, a matsayin abokin takararsa ba, saboda yana son wanda zai yi aiki da shi cikin aminci.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da Arise TV ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel