Zaben 2023: Atiku yana ruwa, magoya bayan Wike sun fara barazana a kan dauko Okowa

Zaben 2023: Atiku yana ruwa, magoya bayan Wike sun fara barazana a kan dauko Okowa

  • An fara surutai bayan zaben Ifeanyi Okowa a matsayin ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa
  • Wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP sun soki wannan mataki da aka ji Alhaji Atiku Abubakar ya dauka
  • Na-kusa da Nyesom Wike sun zargi Atiku da sabawa jam’iyya, suka ce hakan zai yi tasiri a 2023

Rivers - Wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP na jihar Ribas sun soki zabin da Alhaji Atiku Abubakar ya yi na dauko Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takaransa.

Legit.ng ta samu labari cewa wadannan masu ruwa na jam’iyyar hamayyar sun fito su na zargin Atiku Abubakar da kin girmama abin da PDP ta yanke.

Shugaban karamar hukumar Ikwerre a jihar Ribas, Dr. Samuel Nwanosike ya ja-kunnen ‘dan takaran da cewa zai ga tasirin wannan danyen zabi na sa.

Kara karanta wannan

Gwamna Okowa ya yi magana kan dalilin daukarsa da Atiku ya yi maimakon ya zabi Wike

Dr. Nwanosike yake cewa Atiku Abubakar bai girmama jam’iyya ba saboda ya ki daukar zabin kwamiti na musamman da aka kafa domin wannan aiki.

Duk wanda ya saye rariya, ya san za ta zubar da ruwa

An rahoto Nwanosike ya na kawo wani karin magana na mutanen Neja-Delta da yake cewa duk wanda ya sunkumi doya, ya san zai bukaci ruwan sha.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku Abubakar da Nyesom Wike
Atiku Abubakar da Nyesom Wike Hoto: Atiku/Nyesom Wike
Asali: Facebook

‘Dan siyasar yace dole ne wanda ya ci kwanon doya, ya nemi ruwa, idan ba haka ba, zai shake.

Atiku ya saba alkawari

“Idan da ya cika alkawari na yin aiki da abin da jam’iyya ta yanke, da ya bi zabin kwamiti wanda shugaban jam’iyya na kasa da mutanensa suka kafa.”

- Dr. Samuel Nwanosike

Za a gani a zaben 2023

Nwanosike ya yi ikirarin duk masu ruwa da tsaki sun nuna Nyesom Wike ya fi cancanta ya zama abokin takarar Atiku, amma shi ya nuna lallai Okowa yake so.

Kara karanta wannan

2023: Jerin abubuwa 5 da su ka jawo Atiku ya ki daukar Wike, ya zabi Okowa a PDP

Ya ce dagewar da ‘dan takaran ya yi a kan Gwamna Okowa, zai taba PDP a zaben shugaban kasa.

Shi kuma tsohon ‘dan majalisar tarayya na yankin Etche-Omuma, Hon. Ogbonna Nwuke ya ce Atiku Abubakar ya yi watsi da Jihar Ribas ne ba Gwamna Wike ba.

Yayin da Nwanosike ya ce yanzu ya rage a saurari martanin jama’a a wajen zaben 2023. Shi kuwa Nwuke ya ce nan gaba Mai gidan na su zai yi wa Duniya magana.

Wike ba zai ji haushi ba - Okowa

Dazu an ji Gwamna Ifeanyi Okowa ya bayyana abin da zai faru da Nyesom Wike tun da ya rasa zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasan PDP a zaben 2023.

Ifeanyi Okowa yake cewa abin da ya sa Atiku Abubakar ya zabe shi uu yi takara tare a maimakon Wike shi ne dole mutum daya tal za a dauka ya rike wannan kujera.

Kara karanta wannan

Faston da ya saba hasashen zabe ya ambaci ‘Dan takara 1 da ba zai kai labari a 2023 ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel