2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

  • Ana tsaka da neman ganin an zabi wanda zai zama abokin tafiyar Bola Tinubu a matsayin mai rike da tutar jam'iyyar APC a zaben 2023, hadimin gwamnan jihar Kano ya ce ubangidansa be yafi cancanta
  • Ya fadi hakan ne yayin zantawa da manema labarai a karshen mako a Kano, inda ya ce a halin yanzu Ganduje ne kawai zabin da jam'iyyar ke dashi, duba da irin nagarta da halin dattakunsa da ya nuna
  • Ya kara da cewa, Ganduje ne kadai wanda ya fito karara ya marawa Asiwaju baya duk da yadda wasu masu rike da mukaman arewa suka ji tsoron yin hakan, sannan bai da kabilanci tunda har ya dauki 'diyarsa ya ba bayarbe aure

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - Ana tsaka da neman ganin waye dai zama mataimakin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, mai rike da tutar takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, mai bada shawara ta musamman ga Abdullahi Umar Ganduje a kafafan sada zumunci, Shehu Isa ya bayyana dalilan da yasa ya ke ganin ya kamata jam'iyyar da Tinubu su dauki Ganduje a matsayin abokin tafiyarsa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki

Isa wanda ke kokarin ganin ya gamsar da cewa bai saba doka ba tikitin Musulmi da Musulmi, inda ya ce Ganduje ne yafi cancantar rike tutar takarar shugaban kasa a jam'iyyar baya ga Tinubu.

2023: Hadimun Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu
2023: Hadimun Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Vanguard ta ruwaito cewa, hadimin ya fadi hakan ne yayin zantawa da manema labarai a Kano karshe sati.

A cewarsa Isa, "Idan za a yi dubi da irin mahimmanci, kafa tarihi a lokacin aiki, siyasa da irin dattakun da ya ke da shi, Ganduje ne kadai zabin da APC ke da shi.
"Ganduje ne a gaba daya arewa wanda ya fito karara ya tsayawa kamfen din Tinubu duk da irin kalubalen kin amincewa da shi da mutane da dama za su iya, yayin da masu rike da mukamai na arewa suka ji tsoron fitowa fili su mara masa baya.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

"Bai da kabilanci, duk da kasancewarsa Fulani, ya bai wa bayarbe auren 'diyarsa. Ko Tinubu zai fi samun natsuwa yin aiki tare da shi a matsayin abokin tafiyarsa.
"Idan aka dauki Ganduje a matsayin mataimakin shugaban kasa, tabbas zai yi kokarin kawo karshe matsalolin makiyaya, masu garkuwa da mutane, ta'addanci da sa sauran munanan ayyukan da ke addabar kasar nan kasancewarsa kakakin bafulatani," a cewarsa.
"Game da kalubalen tikitin Musulmi da Musulmi, Isa ya ce, hakan baya cikin kundin tsarin mulki, amma Kaduna ta fara gwada wa kuma tun daga lokacin nan, jihar na zaune cikin kwanciyar hankali, ba tare da rikicin kabilar da aka san jihar da shi ba,"

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng