Karshen tika-tiki: Kakakin kungiyar kamfen din Tinubu ya bayyana daga yankin da abokin takararsa zai fito

Karshen tika-tiki: Kakakin kungiyar kamfen din Tinubu ya bayyana daga yankin da abokin takararsa zai fito

  • Kakakin kungiyar kamfen din Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya ce abokin takarar Tinubu na iya fitowa daga arewa maso gabas, arewa maso yamma ko arewa ta tsakiya
  • Ya kuma bayyana cewa ana iya zabar mataimakin shugaban kasar da zai jera da Tinubu daga kowani bangare na addini
  • Sai dai kuma, Onuga ya ce gwamnonin jam’iyyar APC na da yancin zabar wanda ya cancanta a matsayin abokin takara

Kakakin kungiyar kamfen din Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnonin jam’iyyar APC na da yancin zabawa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar abokin takara.

Da yake zantawa da jaridar The Punch, Bayo Onanuga, kakakin kungiyar kamfen din ya bayyana cewa abokin takarar Tinubu zai fito ne daga kowani bangare na yankin arewa kuma zai iya kasancewa daga kowani addini.

Kara karanta wannan

Tinubu zai shiga farautar Mataimakinsa gadan-gadan, watakila a tsaida Gwamna mai-ci

Karshen tika-tiki: Kakakin kungiyar kamfen din Tinubu ya bayyana daga yankin da abokin takararsa zai fito
Karshen tika-tiki: Kakakin kungiyar kamfen din Tinubu ya bayyana daga yankin da abokin takararsa zai fito Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Onuga ya ce zai iya fitowa daga arewa maso gabas, arewa ta tsakiya ko kuma arewa maso yamma, kamar yadda jarida The Cable ta rahoto

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Mataimakin shugaban kasar na iya fitowa daga kowani yanki da addini. Amma kungiyar gwamnonin APC na da yancin zabar mutum. Har zuwa yanzu, duk mun san cewa Atiku bai zabi abokin takara ba.
“Duk da haka, an zabe shi kafin shi. Amma a namu lamarin, harka ce ta jam’iyya.
“Shugabannin jam’iyya za su duba damammakin sannan su yanke shawarar yadda za su daidaita Musulmin da ya fito daga kudu, watakila da mutumin da ya fito daga arewa maso gabas, arewa ta tsakiya ko daga arewa ta yamma. Haka ake yi. Ba zan iya kerewa jam’iyyar ba.
“Kungiyar gwamnonin APC da Gwamna Atiku Bagudu ke jagoranta ita ke da alhakin zaba masa mataimaki da ya cancanta. Dama yana da kyakkyawar alaka da kusan dukkaninsu. Kuma ya kamata ku fahimci cewa bai dade da daukar tikitin shugaban kasar ba.

Kara karanta wannan

An yi zalunci: Tawagar Yahaya Bello ta caccaki shugabannin APC bisa zaban Tinubu

“Na kuma tabbata cewa zabar dan takarar da ya cancanta a matsayin mataimakin shugaban kasa zai kasance a zukatan shugabannin jam’iyyar da ma gwamnonin na APC.
“A halin yanzu, kawai muna so mu dan tsaya sannan mu huta daga gajiyan kamfen din da aka kammala kwanan nan.”

Ganduje: Nasarar Tinubu a APC Alama Ce Da Ke Nuna Ya Samu Karbuwa a Arewa

A gefe guda, Abdullahi Ganduje, gwamnan Jihar Kano, ya taya Asiwaju Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas, murnar samun nasarar lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam'iyyar APC, rahoton The Cable.

Tinubu ya samu kuri'u 1,271 inda ya doke abokan fafatawarsa a zaben na fidda gwani da aka kammala a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

A cikin wata sanarwa da Abba Anwar, babban sakataren watsa labarai, Ganduje ya ce nasarar da Tinubu ya samu a zaben fidda gwanin alama ce da ke nuna ya samu karbuwa a arewa.

Kara karanta wannan

Najeriya ta Dawo Hayyacinta, Za mu batar da Makasan Jama'a, Tinubu Ya Sha Alwashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel