Yanzu: Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Taron Sirri Bayan Nasarar Tinubu A Zaben Fidda Gwanin APC

Yanzu: Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Taron Sirri Bayan Nasarar Tinubu A Zaben Fidda Gwanin APC

  • Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar PDP ya gana da gwamnonin jam'iyyar na PDP a Abuja
  • An yi taron ne a ranar Laraba jim kadan bayan jam'iyyar APC mai mulki a kasa ta kammala zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa kuma Bola Tinubu ya yi nasara
  • Majiya ta bayyana cewa abubuwan da za a tattauna a taron ya kunshi batun zabo wanda zai yi wa Atiku mataimaki da yadda PDP za ta kwace mulki hannun APC a zaben 2023

FCT, Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, a halin yanzu ya shiga wani taro mai muhimmanci da wasu gwamnonin PDP a Abuja.

An sanar da taron ne mintuna kadan bayan nasarar tsohon gwamnan Jihar Legas, Asiwaju Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

Yanzu: Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Taron Sirri Bayan Nasarar Tinubu Zaben Fidda Gwanin APC
Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Taron Sirri Bayan Nasarar Tinubu Zaben Fidda Gwanin APC. Hoto: @atiku.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanzu: Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Taron Sirri Bayan Nasarar Tinubu Zaben Fidda Gwanin APC
Atiku ya shiga taro da gwamnonin PDP a Abuja. Hoto: @atiku.
Asali: Twitter

Daily Trust ta tattaro cewa zaben wanda zai yi wa Atiku mataimaki na cikin manyan abubuwan da za a tattauna a taron.

Wasu abubuwan kuma da za a tattauna ba za su rasa nasaba ba da kwamitin yakin neman zabe, nasarar Tinubu da hanyoyin da za a bi domin tunbuke APC daga mulki a 2023.

Wasu gwamnonin da suka hallarci taron sun hada da gwamnan Jihar Bayelsa, Douyi Diri, Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, Gwamnan Rivers, Nyesom Wike da na Benue, Samuel Ortom.

Saura sun hada da gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da takwararsa na Jihar Oyo, Seyin Makinde.

INEC: Yan Najeriya Na Son Ma'aikatan Mu Su Bi Su Har Gida Su Kai Musu Katin Zabe

A wani rahoto, cikin sabbin masu zabe 34,000 da suka yi rajista daga watan Yuni zuwa Disamba a Legas, 3,000 kawai suka karbi katin zabensu na dindindin (PVC) a cewar kwamishinan zabe na Legas, Olusegun Agbaje.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Kwankwaso Ya Yi Nasarar Zama Dan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Na Jam'iyyar NNPP

Agbaje ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai wurin wani taron wakoki da aka yi don wayar da kan matasa kan zabe a Tafawa Balewa Square Legas, yana mai nuna rashin dadinsa kan rashin karban katin, rahoton Daily Trust.

Ya kara da cewa hukumar ta umurci jami'anta a kananan hukumomi su kira masu zabe su fada musu su taho su karbi katinsu amma ba su samun amsa gamsassu, wasu masu zaben ma cewa suke yi a kawo musu PVC din gidansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel