Kusoshi a Jam’iyya sun dage Tinubu ya dauki Mataimaki daga mutum 2 a Gwamnatin Buhari

Kusoshi a Jam’iyya sun dage Tinubu ya dauki Mataimaki daga mutum 2 a Gwamnatin Buhari

  • Akwai rabuwar kai tsakanin jagororin APC a kan wanda zai yi takarar mataimakin shugaban kasa
  • Bangaren jam’iyyar CPC da suka narke a APC su na so mataimakin Bola Tinubu ya fito daga tsaginsu
  • Yayin da ake kawo shawarar a dauki Kashim Shettima, akwai masu sha’awar Abubakar Malami

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Lokaci ya karaso na zaben ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa, jam’iyyar APC ta na ta lissafin abokin takarar Bola Tinubu.

Wani rahoto da ya fito daga Daily Trust a ranar Talata, 14 ga watan Yuni 2022 ya nuna cewa kai ya rabu tsakanin ‘yan bangarorin da suka taru, aka kafa APC.

Wata majiya ta shaida cewa mutanen tsagin CPC da ke jam’iyyar APC mai mulki za su tunkari shugaba Muhammadu Buhari kan batun tikitin zaben 2023.

Kara karanta wannan

Abokin takara: Atiku na daf da daukar Gwamna mai-ci, Tinubu zai tafi da tsohon Gwamna

Wadannan manya su na shirin haduwa da shugaban kasa da nufin ba shi shawarar ya fadawa Tinubu wanda zai dauka a matsayin ‘dan takarar mataimaki.

Ana kawo mutane 2 a lissafi

Sunayen da wadannan mutane za su kai fadar shugaban kasan sun kunshi Ministocin gwamnatin tarayya; Abubakar Malami da Sanata Hadi Sirika.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Malami SAN shi ne yake rike da kujerar Ministan shari’a na kasa kuma babban lauyan gwamnatin tarayya tun 2015, yana da karfi a gwamnatin nan.

Shi kuma Hadi Sirika shi ne Ministan harkokin jiragen saman Najeriya. Kafin zamansa karamin Minista, ya taba yin ‘dan majalisar wakilai da Sanatan Katsina.

Bola Tinubu
Asiwaju Bola Tinubu mai rike da tutar APC Hoto: @/officialasiwajubat
Asali: Facebook

Amma ana tunanin cewa shugaban kasar zai yi watsi da shawarar mutanen na sa kamar yadda ya yi a wajen zaben ‘dan takaran APC, ya ki goyon bayan kowa.

Jaridar ta rahoto majiyar ta na cewa Buhari zai bar Bola Tinubu ne ya zabi wanda zai yi aiki da shi.

Kara karanta wannan

Atiku yana maganar saida wuta, matatun mai da jirgin kasan Najeriya idan ya karbi mulki

Matsayar Bola Tinubu

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa ‘dan takarar shugaban kasar ya bar wuka da nama a hannun fadar shugaban kasa, a zaba masa duk wanda ya fi cancanta.

Majiyarmu wanda yana da kusanci da wani babban Gwamna a jam’iyyar APC ya shaida mana cewa fadar shugaban kasa ta na so ne Tinubu ya dauki Kirista.

Kingibe ya kawo mutane 3

Dazu kun samu labari cewa Ambasada Babagana Kingibe ya bada sunayen mutum uku; Babagana Umara Zulum; Amina J. Mohammed da Kashim Ibrahim-Imam.

Babagana Kingibe wanda ya yi takarar shugaban kasa a 1993 yana so tikitin APC ya kunshi wadannan mutane da suka fito daga yankin Arewa maso gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel