Yahaya Bello: APC Za Ta Jefa Kanta Cikin Fitina Idan Ta Hana Yin Takara a Zaben Fidda Gwani

Yahaya Bello: APC Za Ta Jefa Kanta Cikin Fitina Idan Ta Hana Yin Takara a Zaben Fidda Gwani

  • Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya ce jam'iyyar APC za ta jefa kanta cikin rikici idan ta hana shi shiga zaben fidda gwani na shugaban kasa
  • Yahaya Bello ya yi wannan jawabin ne a matsayin martani kan matakin da wasu gwamnonin arewa suka dauka na cewa a mika wa kudu mulki a 2023
  • Bello ya ce ba a tuntube shi ba kuma ba adalci bane a hana duk wanda ya cika ka'idan takara shiga takarar, amma ya ce zai iya janye wa idan Shugaba Buhari ya bukaci ya janye

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Talata ya yi gargadin cewa jam'iyyar APC za ta tsinci kanta a rikici idan kwamitin gudanarwa na jam'iyyar ta hana shi yin takara a zaben fidda gwani.

Ya yi wannan gargadin ne yayin da ya ke magana da manema labarai a fadar shugaban kasa, yana mai gwamnonin arewa ba su tuntube shi ba a lokacin da suka cimma yarjejeniyar mika mulki ga kudu, rahoton Channels Television.

Kara karanta wannan

Za ku taro rikici: Yahaya Bello ya fadi abu daya da zai hana shi takara a zaben fidda gwanin APC

Yahaya Bello: APC Za Ta Jefa Kanta Cikin Fitina Idan Ta Hana Yin Takara a Zaben Fidda Gwani
Yahaya Bello: APC Za Ta Jefa Kanta Cikin Fitina Idan Ta Hana Yin Takara a Zaben Fidda Gwani
Asali: Original

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar gwamnan na Kogi, abin da kadai za saka ya janye daga takarar fidda gwani na shugaban na APC shine idan Shuagba Buhari ya fada masa ya janye.

Bello ya ce APC za ta ci zaben shugaban kasa idan ta bi dokoki.

Shugaba Buhari kadai zai iya cewa in janye kuma in amince, Yahaya Bello

A cewar gwamnan na Kogi, abin da kadai za saka ya janye daga takarar fidda gwani na shugaban na APC shine idan Shuagba Buhari ya fada masa ya janye.

Bello ya ce APC za ta ci zaben shugaban kasa idan ta bi dokoki.

A cewar gwamnan na Jihar Kogi, Shugaba Muhammadu Buhari ne kawai zai iya saka shi ya janye daga takarar.

Bello ya ce jam'iyyar APC za ta yi nasara a zaben shugaban kasa idan ta bi dokoki da ka'idoji.

Kara karanta wannan

An kuma: Gwamnoni sun rage yawan 'yan takarar shugaban kasan APC zuwa uku

"Ni mutum ne mai hada kan al'umma; Na nuna hakan sau da dama a jiha na, na nuna hakan sau da yawa a ayyukan da jam'iyya ta ta bani," in ji Bello.
"Babu wanda ya tuntube shi dangane da matakin da su (gwamnonin arewa suka dauka). Zan iya cewa wasu da ke neman kujerar mataimakin shugaban kasa ne ya ja hankalinsu."

Kaduna: Jam'iyyar NNPP Mai Kayan Marmari Ta Zabi Tsohon Sanata A Matsayin Dan Takarar Gwamna

A wani rahoton, Sanata Suleiman Hunkuyi, a jiya ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) bayan samun kuri'un daligets guda 732, rahoton Leadership.

Dan takarar na NNPP zai fafata da Mohammed Ashiru na jam'iyyar PDP da Uba Sani na jam'iyyar APC da wasu yan takarar gwamnan daga wasu jam'iyyu a zaben na 2023.

Hunkuyi ya wakilci mazabar Kaduna North a majalisar dattawa a majalisa zubi ta 8 karkasin APC kafin ya koma PDP a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel