An kuma: Gwamnoni sun rage yawan 'yan takarar shugaban kasan APC zuwa uku

An kuma: Gwamnoni sun rage yawan 'yan takarar shugaban kasan APC zuwa uku

  • Gwamnonin jam'iyyar APC sun rage adadin wadanda za su fafata a zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam'iyyar
  • Wannan na zuwa ne bisa umarnin shugaba Buhari na zakulo wanda ya dace ya gaje shi a zaben 2023 mai zuwa
  • Ya zuwa yanzu dai wasu 'yan takarar na ta bayyana rashin jin dadinsu ga yadda ake shawarin mika mulki Kudu

Abuja - Gwamnonin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) sun kara rage jerin sunayen ‘yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar a zaben fidda gwanin shugaban kasa zuwa uku, rahoton Vanguard.

Da sanyin safiyar Talata ne gwamnonin suka gabatar da jerin sunayen mutane biyar ga shugaban kasa Muhammadu Buhari domin a tantance su saboda a cimma matsaya daya.

Gwamnonin APC sun rage yawan 'yan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC
Yanzu-Yanzu: Gwamnoni sun rage yawan 'yan takarar shugaban kasan APC zuwa uku | Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Wadanda aka fara gabatar da su ga Buhari su ne: ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu; Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Rotimi Amaechi; Gwamna Kayode Fayemi da Gwamna Dave Umahi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Buhari da Gwamna Yahaya Bello sun saka labule a Aso Rock

Sai dai rahotanni sun ce an sake datse jerin sunayen zuwa mutane uku da suka hada da Tinubu, Osibanjo da Amaechi, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai wannan kudiri ba wai wata matsaya ce ba illa shawara ce ga shugaba Buhari da ya bukace su da su taimaka masa wajen rage ’yan takarar guda 23 domin cimma matsaya guda.

Hakazalika, sauran 'yan takara musamman Kayode Fayemi da Yahaya Bello suna ta luguden lebe, suna masu cewa har yanzu suna nan daram kan fafatawar da za a yi a zaben fidda gwanin.

Za ku taro rikici: Yahaya Bello ya fadi abu daya da zai hana shi takara a zaben fidda gwanin APC

A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya gargadi jam'iyyar APC, cewa cire sunansa a jerin 'yan takarar shugaban kasa da za su gwabza a zaben fidda gwani na yau daidai yake yake da kunno wutar rikici, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC sun gabatarwa Buhari jerin sunayen yan takarar shugaban kasa 5

Gwamna Bello, wanda yana daya daga cikin ’yan takara 23 a jam’iyyar, ya ce akwai makarkashiyar da ake shirya masa, inda ya zargi gwamnonin APC na Arewa da wasu jiga-jiga da kitsa manakisa akansa.

Bello wanda ya bayyana kansa a matsayin dan takara mafi karbuwa da zai yi nasara idan har tsarin ya tafi daidai, ya ce abu daya ne zai hana shi ya tsaya takarar shugaban kasa shi ne idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya janye daga takarar, inji The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel