Ta Fasu: Majiyar Cikin Gida Ta Fallasa Sunan 'Dan Takarar da Buhari ya Karkata Hankali Wurinsa

Ta Fasu: Majiyar Cikin Gida Ta Fallasa Sunan 'Dan Takarar da Buhari ya Karkata Hankali Wurinsa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada haske kan wanda ya ke son ya gaje shi a taron da yayi da gwamnonin APC
  • Majiyar cikin gida ta ce amfani da kalmar 'cigaba' da ya yi na nuna karkatar da hankalinsa yayi kan Farfesa Yemi Osinbajo
  • Osinbajo mai shekaru 65 yana daya daga cikin 'yan takara na kan gaba a shugabancin kasa na jam'iyyar mai mulki

Aso Rock - Shugaban kasa Muhammadu Buhari na iya zaben magajinsa kuma ya bukaci a tsayar da 'dan takarar yarjejeniya domin samun tikitin jam'iyyar APC.

Shugaban kasan ya sanar da hakan ne tun ranar Talata, 31 ga watan Mayu a yayin da ya gana da gwamnonin APC da shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu.

Ta Fasu: Majiyar Cikin Gida Ta Fallasa Sunan 'Dan Takarar da Buhari ya Karkata Hankali Wurinsa
Ta Fasu: Majiyar Cikin Gida Ta Fallasa Sunan 'Dan Takarar da Buhari ya Karkata Hankali Wurinsa. Hoto daga Buhari Sallau
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo yana daya daga cikin manyan 'yan takara na sahun gaba a jam'iyyar APC. Majiyoyin cikin gida na jam'iyyar APC sun sanar da Legit.ng cewa shugaban kasan hankalinsa ya fi karkata kan dan takara daya tak da zai gaje shi.

Kamar yadda majiyar ta ce, amfani da kalmar 'cigaba' da shugaban kasan yayi ya nuna cewa hankalinsa ya fi karkata ga mataimakin sa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Majiyoyi daga fadar shugaban kasan suna ta amfani da wannan kalmar wurin nuna goyon bayansu ga mataimakin shugaban kasan wanda ya tara magoya baya masu dumbin yawa tun bayan da ya bayyana burinsa na gaje ubangidansa.

Majiyar wacce ta halarci taron ta kara da cewa gwamnonin sun sanar da shugaban kasan cewa za su tafi tattaunawa bayan ya bayyana matsayarsa a taron.

Buhari ya yi bayanin cewa, tuni APC ta kafa tsarikan cikin gida da za su inganta cigaba da kuma tsarikan mulki a matakan jiha da kananan hukumomi.

A kalamamsa: "A misali, gwamnonin da wa'adin mulkinsu na farko ya kare kuma suka yi kwazo, an shawarce su da su sake neman kujerar. Hakazalika, gwamnonin da wa'adin mulkinsu na biyu ya kare, an ba su damar su bayyana magadansu da suka san za su iya dasawa daga inda suka tsaya tare da kare mutuncin jam'iyyar."
Majiyar ta ce a yayin bayani kan yadda jam'iyyar ta karfafa guiwoyin gwamnonin da wa'adin mulkinsu na farko ya kare da su nemi zarcewa, "Shugaban kasa ya yi kira kan zaben mutum daya da zai rike tutar jam'iyyar kuma ya bayar da satar amsa kan wanda ya fi so ya gaje shi ta hanyar ambatar cigaba daga inda ya tsaya ta mataimakinsa."

Mutanen Bola Tinubu sun bukaci wasu ‘yan siyasa 3 su gaggauta janye takarar Shugaban kasa

A wani labari na daban, kwamitin yakin neman zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nemi ‘yan siyasan Arewa da ke neman tikitin zama shugaban kasa a APC su hakura.

The Cable ta ce kwamitin yakin zaben ya na so Dr. Ahmad Lawan, Yahaya Bello da Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura su bar maganar neman takaran 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel