Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC

Legit.ng na ta kawo muku yadda zaben ke gudana kai tsaye daga filin wasa na Eagle Square da ke babban birnin tarayya na Abuja.

An fara kirga ƙuri'u

Bayan kammala tantance kuri'un da aka kaɗa a taron fidda ɗan takarar shugaban kasa na APC, kwamitim zaɓe ya fara ƙirga kuri'un da kowane ɗan takara ya samu.

Ga su kamar haka:

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi = 38

Fastor Tunde Bakare = 0

Sanata Ahmed Sani Yerima = 4

Emeka Nwajuiba = 1

Rotimi Amaechi = 316

Farfesa Yemi Osinbajo = 235

Jack Rich = 0

Ogbonnaya Onu = 1

Gwamna Yahaya Bello = 47

Sanata Ahmed Lawan = 152

Sanata Rochas Okorocha = 0

Gwamna Ben Ayade = 37

Ikeobasi Mokelu = 0

Shugaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo sun dawo Eagle Square

Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, sun koma farfajiyar Eagles Square yayinda kirgan kuri'un da aka kada ya zo karshe.

Sakamakon zaben kawo yanzu

Bola Ahmed Tinubu- 1070

Rotimi Amaechi-238

Yemi Osinbajo-177

Ahmed Lawan-102

Yahaya Bello- 25

Dave Umahi-20

Ben Ayade-21

Ahmed Sani-3

Masoya Tinubu na ta kodimo, ana ta ambatan sunansa

Yayin da ake ci gaba da kirgan kuri'u, masoya Tinubu sai murna suke, inda ake ci gaba da ambato sunan Tinubu a matsayin na gaba-gaba a zaben fidda gwanin APC.

Ya zuwa yaznu dai an akwatuna hudu ne aka kirga, kuma Tinubu na kan ganiyar nasara.

Tinubu ne kan gaba a kuri'un da aka tantace

Tsohon gwamnan jihar Lagas, Bola Tinubu, ne kan gaba da yawan kuri'u aka soma kirgawa domin tantace yawan kuri'un da kowanne dan takara ya samu.

Ana ta ambatan sunan Tinubu yayin da wadanda suka shirya zaben fidda dan takarar shugaban kasar jam’iyyar a Eagle Square ke tantance akwatunan zabe biyu, Vanguard ta rahoto.

An fara shirin tantance kuri’un da aka kada

A yanzu haka, ana shirin tantance kuri’un da deliget suka kada domin sanar da wanda ya yi nasarar lashe zaben fidda gwanin na APC.

An gano wakilan zabe dauke da akwatunan kuri’un da aka kada yayin da dandanzon jama’a da jami’an tsaro suka sanya su a tsakiya.

Yanzu Yanzu: An gama kada kuri’a

An kammala kada kuri'a a babban zaben fidda gwanin shugaban kasa na jam'iyyar APC.

Zaben, wanda aka fara da misalin karfe 2:00 na tsakar dare, ya zo karshe da karfe 7.45 na safiyar Laraba kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Dukkan deliget ddin ihohi 35 da na FCT sun kada kuri'unsu, deliget din jihar Akwa Ibom ne kadai ba su yi zabe ba sakamakon umarnin kotu.

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

Magoya bayan Tinubu sun fara murna tun kafin gama zaɓe

Magoya bayan jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sun fara tiƙa rawa a filin taron yayin Deleget ke cigaba da kaɗa kuri'u a Eagle Square.

Kalli Bidiyon anan:

Deleget na cigaba da kaɗa kuri'u

Barkan mu da safiya, Legit.ng zata cigaba da kawo mutu abubuwan da ke wakana daga Filin taron APC na zaɓen fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa, tuni dai wakilai suƙa fara kaɗa kuri'un su.

Zuwa yanzun Deleget na jihohi kusan 30 sun kammala kaɗa kuri'un su, ana tsammanin kammala zaɓen nan ba da jimawa ba, bayan haka tantancewa da ƙirga kuri'u zai biyo baya.

Akwatunan zaɓe a wurin taron APC.
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC Hoto: eruditeblog/facebook
Asali: Facebook

Mace daya tilo dake takara, Uju Ohanenye, ta janyewa Bola Tinubu

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Asali: UGC

Nicholas Felix ya janyewa Yemi Osinbajo

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Asali: Twitter

Sanata Ajayi Borrofice ya janyewa Bola Tinubu

Sanata Ajayi Borrofice ya janyewa Bola Tinubu

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC

Gwamnan jihar Jigawa, Badaru Talamiz, ya janyewa Bola Tinubu

Gwamnan jihar Jigawa, Badaru Talamiz ya janyewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Asali: UGC

Tsohon Kakakin majalisa ya janyewa Tinubu

Tsohon Kakakin majalisar wakilan tarayya, Oladimeji Bankole, ya janyewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Asali: UGC

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya janyewa Bola Tinubu

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya bi sahun tsaffin gwamonin biyu, ya janyewa Asiwaju Bola Tinubu

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Asali: Facebook

Ibikunle Amosun ya janyewa Bola Tinubu

Tsohon Gwamnan jihar Ogun ya Janyewa Bola Tinubu

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Asali: UGC

Akpabio ya janye daga takara, ya marawa Tinubu baya

A ci gaba da zaben fidda gwanin APC, dan takarar APC daga kudu ya janye, ya marawa Bola Ahmed Tinubu baya.

Hotunan Shugaba Muhammadu Buhari yayinda ya dira Eagle Square

Bidiyon yadda deliget din Lagas suka yiwa Osinbajo ihun bama yi a filin Eagle Square

Daliget din Lagas sun yiwa mataimakin shugaban kasa kuma dan takara a zaben fidda gwanin APC, Yemi Osinbajo ihun bama yi a wajen taron na Eagle Square.

A cikin wani bidiyo da ya bayyana daga wurin taron, an jiyo su da wasu dandazon mutane suna ihun ‘hoooo’ yayin da wasu kananan maganganu ke tashi daga kasa.

Gwamnan jihar Kaduna, El-Rufa'i, ya dira tare da tawagarsa

Zamu fara yunkuro wa daga yau - Shugaban APC

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce abubuwa ba su dagulewa APC ba kuma daga yau matakan farfaɗowa zasu fara.

Adamu, yayin jawabi a munbarin filin Eangle Square kafin fara zaben fidda gwani ya ce komai na tafiya yadda ya kamata kuma kan ƴaƴan jam'iyga a haɗe yake.

Shugaban APC na ƙasa.
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban kasa ya hallara a filin Eagle Square

Mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar da ke fatan lashe tikitin APC, Farfesa Yemi Osinbajo, ya isa filin babban taron APC na musamman wanda Deleget zasu yanke magajin Buhari.

Jagaban, Bola Ahmed Tinubu, ya dura babban filin taron APC

Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya isa filin Eagle Square inda za'a fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC.

Tinubu na ɗaya daga cikin yan takara na sahun gaba da ake tsammanin zasu iya lashe tikitin zama magajin Buhari a 2023.

Kalli bidiyon a nan

Uwai gidan shugaban ƙasa Aisha Buhari ta dira Eagle Square

Uwar gidan shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, yanzu haka tana cikin filin Eagle Square yayin da ake gab da fara zaɓen fidda gwanin APC.

Bayan ita manyan jiga-jigan siyasa a Najeriya sun hallara, shugaban majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya isa filin taron.

Vanguard ta tattaro cewa gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, ya dira filin taron. Yanzu dai ana jiran fara zaɓe.

Filin taron APC.
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira Eagle Square

Shugaba Muhammadu Buhari ya dira farfajiyar Eagle Square don musharaka a zaben fidda gwanin yan takaran kujerar shugaban kasa na APC.

Yanzu da Buhari ya iso, za'a bude taro.

Wani bidiyo da gidan talabijin na Channels ya yada ya nuna lokacin da Buhari ke shigowa filin.

Kalli bidiyon:

Jiga-jigan APC na dira farfajiyar Eagle Square

Mataimakin shugaban kasa, Shugaban majalisar dattawa, tsohon ministan sufuri, karamin ministan man fetur, shugaban uwar jam'iyyar APC, Ahmad Sani Yarima, da sauran jiga-jigai sun dira farfajiya.

Hakazalika uwargidar shugaba Buhari, Aisha Muhammadu, ya dira wajen.

Yanzu Shugaba Buhari ake jira.

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Asali: Original

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Asali: Original

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Asali: Original

Jami'an tsaro mata sun ba hammata iska a wurin taron APC

Jami'an tsaro mata daga hukumar yan sandan kasar na da kuma hukumar NSCDC sun bai wa hammata iska a filin taron jam'iyyar APC na zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa.

Gwamna Yahaya Bello ya faso wurin taron

Gwamnan jihar Kogi kuma daya daga cikin masu neman takarar kujerar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam’iyyar APC, Yahaya Bello ya isa wurin taron.

An gano Bello tare da jami’an tsaro da wasu mukarrabansa yayin da yake dagawa taron jama’a hannu.

Hakazalika jami'an hukumar EFCC sun kasance a wajen taron domin zuba idanu kan yadda hada-hadar kudi ke gudana ta yanar gizo

Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya isa filin taro

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya isa filin babban taro Eagle Square wanda za'a zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023 karkashin APC.

Gwamna Babagana Zulum da takwaransa Bello Matawalle sun hallara a wurin taron

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum da takwaransa na jihar Zamfara, Bello Matawalle, sun bi sahun sauran mambobin jam’iyyar APC zuwa filin babban taronsu.

Hakazaila an gano Fasto Tundu Bakare tare da tsohon shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomhole a waurin.

Ana sanya ran shugaban kasa Muhammadu Buhari ma zai isa wajen ba da jimawa ba kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.

Gwamnan Imo ya isa wurin taron APC

Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya dira filin babban taron jam'iyyar APC na zaɓen ɗan takarar shugaban kasa tare da jerin gwanon motocinsa.

Deleget na jihar Osun sun dira Eagle Square

Wakilan jihar Osun sun dira farfajiyar Eagle Square bayan kammala tantancesu a ICC.

Rikici ya kaure a wurin tantance Deleget

Rikici ya kaure a wurin tantance Deleget bisa zargin yunƙurin canza ma'aikatan wucin gadi da aka tanaza musamman saboda babban taron zaɓen fidda gwanin APC.

Jaridar The Cable ta gano cewa jam'iyya ta bai wa wasu matasa horo na musamman domin wannan taron, amma kawai sai aka sauya su yau Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ne ya sa baki kuma ya warware matsalar.

Haka zalika wasu bayanai sun nuna cewa an yi yunƙurin sauka sunaye Deleget domin taimaka wa shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan.

An fara tantance deliget da za su kada kuri’a

A yanzu haka, an fara tantance deliget da za su kada kuri’a a zaben fidda dan takarar shugaban kasar na APC a cibiyar taro ta kasa da ke Abuja.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa an kwashi deliget din zuwa wajen tantance su ne a cikin motocin bas da aka tanada domin hakan.

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC Hoto: The Nation
Asali: UGC

Yan jaridu sun yi cirko-cirko a kofar shiga filin taro

Bayanan da muke samu yanzu sun nuna cewa har zuwa yanzun yan jaridun da aka ware domin aikin ɗakko abun da ke faruwa a filin taron APC ba su samu damar shiga ba.

Daily Trust ta rahoto cewa hakan ta faru ne bisa gazawar Kwamitin midiya da yaɗa labarai karkashin gwamna Abdullahi Sule na raba musu takardar shaidar aiki 'Tags' kafin shiga filin.

Tun mako biyu kafin yau, gidajjen jaridu suka rubuta takarda zuwa Ofishin labarai na APC domin samun sahalewar jam'iyya na aiki ranar taro.

Yan jaridun da suka isa Eagle Square tun da safiyar yau Talata na cigaba da dako sakamakon jami'an tsaro sun hana su shiga wurin.

Kofar filin taron APC a Abuja.
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Deliget din Kwara sun shirya tsaf don marawa Tinubu baya

Jaridar The Nation ta rahoto cewa farin ciki ya kaure a tsakanin deliget din jihar Kwara game da bukatar da gwamnoni suka gabatar na cewa a bari yan takara biyar su kara a zaben fidda gwanin.

Deliget din, wadanda ke goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu, sun jadadda jajircewarsu kan takarar tsohon gwamnan na jihar Lagas.

Wani deliget ya ce:

“Allah ya albarkaci gwamnanmu, AbdulRasaq, wanda bai kasance mai hayaniya ba. A karkashin shugabancinsa, muna goyon bayan babban jagoranmu na kasa, wanda ke ta wanzar da zaman lafiya da sasanci a Kwara. Yana son mu. Za mu Eagle Square domin saka masa da soyayyar da ya nunamana. Allah ya albarkaci gwamnanmu. Allah ya albarkaci Asiwaju.”

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Babu masaka tsinke a wasu hanyoyin Abuja

Motoci da sauran ababen hawa sun cika hanyoyin Abuja sakamakon babban taron APC na zaben ɗan takarar shugaban kasa.

Daily Trust ta rahoto cewa duk da taron na gudana ne a filin Eagle Square amma jami'an tsaro sun rufe wasu hanyoyi, hakan ya haddasa cunkoso kuma ya jefa mutane cikin wahalhalu.

Wasu daga cikin hanyoyin da cunkoson ya dabaibaye sun haɗa da hanyar Goodluck Ebele Jonathan Road, ECOWAS ta wajen ma'aikatar harkokin mata, bayan ma'aikatar harkokin kasashen waje da sauran su.

Wasu Hotuna sun nuna yadda Motoci ke canza hanya biyo bayan rufe wasu hanyoyi, sanadin rashin wadatar hanyoyi ya haddasa cunkuson.

Cunkoson ababen hawa a wasu hanyoyin Abuja
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC Hoto: Oma Arona/facebook
Asali: Facebook

Hanyoyi ba masaka tsinke a Abuja.
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC Hoto: Oma Anona/facebook
Asali: Facebook

Za a fara kada kuri’a da misalin karfe 6:00 na yamma sannan za a sanar da wanda ya lashe zaben da karfe 10:00 na dare

Jaridar The Cable ta rahoto cewa za a fara kada kuri’a don zabar dan takarar shugaban kasa da zai daga tutar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da misalin karfe 6:00 na yammacin yau Talata.

An shirya fara babban taron na APC ne a hukumance da misalin karfe 10:00 na safiyar yau Talata, 7 ga watan Yuni.

A bisa ga jadawalin taron da jam’iyyar ta saki, shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Adamu, zai gabatar da jawabin maraba da zuwa da misalin karfe 3:40 na rana.

Za a ba masu neman takarar shugaban kasa damar gabatar da jawabansy na godiya a tsakanin karfe 4:45 da 5:45 na yamma.

Bayan nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabinsa da misalin karfe 5:45.

Deliget za su fara kada kuri’arsu daga karfe 6:00 na yamma zuwa karfe 9:00 na dare, yayin da za a sanar da sakamakon da misalin 10:00 na dare.

Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC
Kai Tsaye: Yadda ake Gudanar da Zaɓen Fidda Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na APC Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Komai daidai, cikin natsuwa yayin da 'yan jarida ke jiran a tantance su

A rana ta biyu na taron zaben fidda gwanin shugaban APC, 'yan jarida sun taro domin samun daman shiga harabar filin taro na Eagle Square.

Wasu hotunan da muka samo daga jaridar Daily Trust sun nuna lokacin da 'yan jarida ke jira domin a tantance su.

Kalli hotunan:

Bayan kai ruwa rana kan tsayar da ɗan takarar Masalaha, Deleget zasu raba gardama yau

Barkan mu da sake saduwa a rana ta biyu daga cikin ranakun da jam'iyyar APC ta tsara gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar shugaban ƙasa, duk wasu shirye-shirye a filin Eagle Square sun kammalu.

A yau Talata ne ake tsammanin Deleget zasu zabi wanda zai riƙe tutar APC a zaɓen shugaban kasa da ke tafe. Sai dai a ranar Litinin an kai ruwa rana a APC kan tsayar da ɗan takarar maslaha.

Mambobin Kwamitin NWC na APC ta ƙasa sun rabu bayan shugaban jam'iyya, Sanata Abdullahi Adamu, ya sanar msusu cewa Sanata Ahmad Lawan ne ɗan takarar maslaha. Hakan ya jawo kace-nace daga masu ruwa da tsakin APC.

Gwamnonin arewa sun sake jaddada matsayar su cewa tilas a kai mulki Kuudi, mambobin NWC suka mara musu baya.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar jiya Litinin, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce babu wanda zai ƙaƙaba ɗan takara a bar Deleget su yanke hukunci. Buhari ya ce bai zaɓi kowane ɗan takara ba.

Ko APC zata gano bakin zaren ta iya fitar da ɗan takarar da kowa zai aminta da shi? Legit.ng zata cigaba da kawo muku dukkan abubuwan da ke wakana a wurin taron APC na musamman.

Jami’an tsaro sun hana ma’aikatan gwamnati shiga

Jami’an tsaro sun hana ma’aikatan gwamnati shiga ofishoshinsu saboda kusancinsa da filin babban taron na jam’iyyar APC.

Online view pixel