Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

 • A yau ne jam'iyyar APC ta fara atisayen tantance 'yan takarar da zasu gwabza a zaben fidda gwaninta na makon nan
 • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyar ke daukar dumi kan wanda zai fito ya gaji Buhari a zaben 2023
 • Ya zuwa yanzu, rahotanni sun ce akalla mutane tara ne suka tsallake tantancewar shugabannin jam'iyyar APC

Abuja - Bayan kwashe makwanni ana shirye-shiryen gudanar da babban taron zaben fidda gwani na shugaban kasa, ga dukkan alamu al’amura sun fara tafiya a jam’iyyar APC mai mulki inda a karshe ta fara tantance ‘yan takararta na shugaban kasa a yau Litinin.

Jam'iyyar wadda ta ci gaba da yin taron a cikakken sirri ta kuma hana 'yan jarida zuwa wurin taron.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 zai iya zama Gwamnan da ya yi takara da shi

Shugaban kwamitin tantancewar kuma tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Cif John Odigie-Oyegun bai amsa tambayoyin da wakilin Vanguard ya yi masa ba game da taron.

Ana ci gaba da tantance 'yan takarar APC a Abuja
APC: Tinubu, Badaru, da wasu 9 sun tsallake tantancewar shugabannin APC | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da jigo a jam’iyyar, Sanata Ali Modu Sheriff ya yi tir da wadanda suka kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa ta hanyar sanya hotunansa a wurare masu mahimmanci a fadin babban birnin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka kuma, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu a ranar Litinin a sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa ya yi wata ganawar sirri da shugabanta na kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Ko da yake bai yi magana da ‘yan jarida ba, amma ta kara rura wutar rade-radin sauya shekarsa biyo bayan rashin nasarar da ya samu a zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Enugu.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen sanatoci 42 da ba lallai su koma majalisar dattawa ba a 2023

Wadanda suka tsallake tantancewar shugabannin APC

Bayanai da aka samo sun tabbatar da cewa 12 daga cikin 25 masu neman shugabancin kasar nan a APC sun tsallake atisayen tantancewa daga shugabannin jam'iyyar, inji rahoton Daily Sun.

Ga jerin wadanda aka tantance a yau Litinin:

 1. Chukwuemeka Nwajiuba, tsohon karamin ministan ilimi
 2. Abubakar Badaru, gwamnan Jigawa
 3. Uji Kennedy Ohanenye ('yar takara mace tilo)
 4. Pastor Tunde Bakare
 5. Sanata Robert Ajayi Borroffice
 6. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
 7. Dave Umahi, gwamnan jihar Ebonyi
 8. Sanata Ibikunle Amosun, tsohon gwamnan jihar Ogun
 9. Felix Nicholas
 10. Ken Nnamani
 11. Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri
 12. Sani Yerima, tsohon gwamnan Zamfara

Wadanda za a tantance ranar Talata

 1. Dimeji Bankole
 2. Kayode Fayemi
 3. Godswill Akpabio
 4. Yemi Osinbajo
 5. Rochas Okorocha
 6. Yahaya Bello
 7. Tein Jack-Rich
 8. Christopher Onu
 9. Ahmad Lawan
 10. Ben Ayade
 11. Ikeobasi Mokelu

Babbar magana: An bukaci kwamiti ya kori Tinubu daga takaran shugaban kasa a APC

A wani labarin, an bukaci kwamitin tantance 'yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC da ya kori Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas, saboda alamomin tambaya game cancantar iliminsa, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takara a PDP ya lashe tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour

A wata wasika mai dauke da kwanan watan Mayu 17, 2022, wani Sagir Mai Iyali, wanda ya bayyana kansa a matsayin dan APC daga jihar Kano, ya roki jam’iyyar da ta haramtawa Tinubu takara kan wasu takardun karya da ya mika wa INEC a 1998.

John Oyegun, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ne ke jagorantar kwamitin tantancewar, kuma ana ci gaba da atisayen ne a Transcorp Hilton da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel