2023: Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Takarar APC 2 Saboda Sun ƙi Janye Wa Wani Ɗan Takarar

2023: Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Takarar APC 2 Saboda Sun ƙi Janye Wa Wani Ɗan Takarar

  • Yan sanda a Jihar Ebonyi sun kama wasu yan takara biyu, yaya da kani a yayin zaben fidda gwani na jamiyyar APC a jihar
  • Barista Rollins Offia Nwali da dan uwansa Injiniya Alfred Offia Nwali sun yi ikirarin cewa an kira su daga gidan gwamnati su janye takara amma suka ki shi yasa aka kama su
  • Wata majiya na kusa da Rollins da Alfred ta tabbatar da cewa yan sandan sun kama su ne suka kuma tarwatsa magoya bayansu da daliget a yayin zaben fidda gwanin

Ebonyi - Yan sanda a jiya a Jihar Ebonyi sun kama 'ya'yan daya daga cikin dattawan da suka kafa Jihar Ebonyi, marigayi Sanata Office Nwali kan zarginsu da kin janye wa wani dan takarar a zaben fidda gwani na APC da aka kammala a jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

Vanguard ta rahoto cewa yan uwan su biyu, Barista Rollins Offia Nwali da dan uwansa Injiniya Alfred Offia Nwali, an kama su ne a ranar Alhamis a Onueke a karamar hukumar Ezza ta jihar.

2023: Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Takarar APC 2 Saboda Sun ƙi Janye Wa Wani Ɗan Takarar
2023: Ƴan Sanda Sun Kama Ƴan Takarar APC 2 Saboda Sun ƙi Janye Wa Wani Ɗan Takarar a Ebonyi. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rollinsa Offia Nwali, dan takarar majalisar jiha ne a zaben fidda gwani na jam'iyyar ta APC.

Yana takarar tikitin wakiltar mazabar Ezza ta Kudu ne kafin a kama shi.

Majiya ta magantu kan yadda abin ya faru da yan siyasan biyu

Wata majiya ta yi ikirarin cewa an kama Mr Nwali ne saboda ya ki ya janye wa abokin hammayarsa a zaben.

"An kira shi sau da yawa daga gidan gwamnatin jihar don ya janye amma ya ce a matsayinsa na dan daya daga cikin wadanda suka kafa jihar, abokin hammaya na ya kamata ya janye min.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

"An kira shi an masa barazana sau da yawa kan zaben amma bai janye ba. Sun kama shi yayin da suka ga zai ci zaben domin mutane da dama za su bi shi zuwa mazabarsa," in ji mazabar.

Majiyar ta cigaba da cewa an fatattaki magoya bayansa daga wurin zaben har ma da wasu daliget kamar yadda Naija Dailies ta rahoto.

Yayan cikin yan uwan biyu, Oguzor Offia Nwali, ya tabbatar da kama su.

Ya kuma yi ikirarin cewa 'masu karfin juya jihar' ne suka son kawar da shi domin dan takarar da suka so ya ci zaben.

"Eh, an kama yan uwa na biyu kuma mun ji cewa an tafi da su hedkwatar yan sanda da ke Abakaliki," in ji shi.

An yi kokarin ji ta bakin kakakin yan sandan jihar, Chris Anyanwu game da lamarin amma ba a same shi ba don wayoyinsa rufe suke a lokacin hada wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamna ya lashe tikitin PDP don sake takarar gwamna a 2023

Katsina Ba Ta Siyarwa Ba Ce, Ɗalibai Ga Wakilan Jam'iyyu

A wani rahoton, Kungiyar Hadin Kan Daliban Jihar Katsina ta shirya zanga-zangar lumana musamman ga wakilan manyan jam’iyyu akan su zabi ‘yan takarar gwamna na kwarai wadanda za su ciyar da jihar gaba.

Daily Trust ta ruwaito cewa daliban sun dinga zagaye manyan titinan da ke garin Katsina rike da takardu wadanda su ka rubuta, “Jihar Katsina ba ta siyarwa ba ce”.

Yayin zantawa da manema labarai, shugaban daliban, Aliyu Mamman, ya nemi wakilan su duba zabin da ke zuciyoyin mutanen jihar wadanda su ka zarce mutane miliyan takwas a zuciyarsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel