Karin bayani: Gwamna ya lashe tikitin PDP don sake takarar gwamna a 2023

Karin bayani: Gwamna ya lashe tikitin PDP don sake takarar gwamna a 2023

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya sake samun damar yin takarar gwamna a karo na biyu a karkashin jam'iyyar PDP
  • Gwamnan ya sanar da lashe zabensa na fidda gwani da jam'iyyar ta gudanar a fadin kasar nan kamar yadda rahotanni suka tabbatar
  • Ya zuwa yanzu dai, jihohi na ci gaba da sanar da sakamakon zabukan fidda gwani da ke gudana a fadin jihohin kasar nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Oyo- Gwamna Seyi Makinde, a ranar Alhamis, ya zama wanda ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan jihar Oyo na jam’iyyar PDP.

A zaben fidda gwani da aka gudanar a filin wasa na Lekan Salami da ke Adamasingba, Ibadan, Makinde ya samu kuri’u 1,040 inda ya doke abokin takararsa Hazeem Gbolarunmi wanda ya samu kuri’u biyu, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Dan Sule Lamido ya lashe zaben fidda gwanin yan takarar gwamnan Jigawa

Gwamna Makinde ya samu damar komawa takara a karo na biyu
Yanzu-Yanzu: Gwamna ya lashe tikitin PDP don sake takarar gwamna a 2023 | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Kamar yadda jami’in zaben ya bayyana, Ben Obi wanda Abdullahi MaiBasia ya wakilta, Makinde ya zama dan takarar gwamnan jihar Oyo a jam’iyyar PDP bayan ya samu mafi yawan kuri'u.

Jimillar kuri'u shida ne marasa kyau daga cikin kuri'u 1,048 da aka kada.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Makinde ya yabawa 'yan jiharsa da suka amince ya ci gaba da aiki daga inda ya tsaya bayan amince dashi a karo na farko bayan 2019, inji rahoton Punch.

Ya zuwa yanzu, jihohin Najeriya na ci gaba da kawo sakamakon zaben fidda gwani da ake ci gaba da gudanarwa, yayin da ake samun matsaloli na rarrabuwar kai a wasu jihohin.

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

A bangare gudam kunji cewa, jam'iyyar adawa ta PDP ta dage zaben fitdda gwani da ke gudana a jihar Neja, biyo bayan wata zanga-zanga da ta barke, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gombe: Bayan shan kaye a APC a 2018, Barde ya dawo PDP, ya samu tikitin gwamna na 2023

Zaben da aka shirya gudanarwa a yau Laraba ya koma Alhamis bayan zanga-zangar da hudu daga cikin biyar da ke takara suka tayar.

Rahoto ya bayyana cewa an fara samun matsala ne yayin da hudu daga cikin biyar din suka nuna rashin gamsuwa da jerin sunayen deliget-deliget da za su kada kuri'a, rahoton Premium Times.

Asali: Legit.ng

Online view pixel