Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

  • Na gaba-gaba a takarar gwamnan jihar Rivers a APC ya sauya sheka a daidai lokacin da ake shirin fara zaben fidda gwani
  • Wannan na zuwa ne bayan zargin da dan takarar ya yi na cewa, akwai makarkashiya a tafiyar da tsarin jam'iyyar
  • Hakazalika, ya kira masoyansa da su kula, kuma kada su bata lokaci wajen halartar zaben da aka shirya manakisa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Rivers - Sanata Magnus Abe ya fice daga jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan. Ya kuma fice daga takarar Gwamna a APC a jiharsa.

The Nation ta ruwaito cewa, Abe ya bayyana janyewarsa daga takara ne ta hannun kodinetan kungiyar kamfen na Bola Ahmed Tinubu Support Vanguard (BATS-V), Sir Tony Okocha na Kudu maso Kudu.

Dan takarar APC ya fice daga takarar gwamnan jihar Rivers
Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye takara, ya fice daga jam'iyyar APC | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Depositphotos

Okocha ya ce duk da ficewa daga jam'iyyar APC, burin zama gwamnan jihar Rivers na Abe na nan daram.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan janyewa daga takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fice daga PDP

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, sanarwar ta ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ina ta samun dimbin kiraye-kiraye daga abokan aikinmu game da zaben fidda gwani na ‘yan takarar gwamna na jam’iyyarmu ta APC.
“Don Allah a dauki wannan a matsayin sanarwa a hukumance cewa ba za mu shiga gurbatacce tsari, na son zuciya, da son kai ba a RIVERS.
“Ana shawartar dukkan masu goyon bayan mu da kada su bata lokacinsu a cikin tsarin da ba zai haifar da da mai ido ba."

2023: Dasuki ya samu takarar Majalisa a PDP, yana goyon bayan Tambuwal a kan Atiku

A wani labarin, Hon. Abdussamad Dasuki shi ne wanda ya yi nasarar zama ‘dan takarar PDP na yankin Kebbe da Tambuwal a majalisar tarayya a zaben 2023.

This Day ta ce tsohon kwamishinan kudin ya samu babbar nasara a zaben tsaida gwanin da jam’iyyar PDP ta shirya a ranar 22 ga watan Mayu, 2022.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

Abdussamad Dasuki ya lashe duka kuri’u 65 da ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP suka kada a zaben tsaida gwanin da aka gudanar kamar yadda sakamako ya nuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel