Abubuwa 7 da suka sa NNPP ta zama jam’iyyar da kowa yake marmari a Kano cikin watanni 2

Abubuwa 7 da suka sa NNPP ta zama jam’iyyar da kowa yake marmari a Kano cikin watanni 2

  • Alamu su na nuna a halin yanzu NNPP ce jam’iyyar hamayyar da ke cin kasuwa a siyasar Kano
  • Wannan ya kara tabbatar da maganar da ake dade ana fada na cewa lallai siyasar Kano sai Kano
  • A farkon shekarar nan ta 2022 kusan babu wanda ya san da zaman jam’iyyar NNPP a jihar Arewan

A wannan rahoto, mun tattaro yadda wannan jam’iyya ta NNPP da ake yi wa lakabi da mai kayan marmari ta zama babbar jam’iyyar adawa a jihar Kano.

Premium Times ta kawo wasu daga cikin dalilan da ya sa jam’iyyar ta yi ‘ya ‘ya da yawa a dan lokaci.

1. Sauya-sheka

A yau babu jam’iyyar da ake shiga cikinta a jihar Kano irin NNPP, duk da akwai APC, PDP da PRP. An samu musamman manya a APC da suka koma NNPP.

Kara karanta wannan

Dadi ya kashe tsohon shugaban yakin neman zaben Tinubu bayan hadewa da Kwankwaso a siyasa

Jaridar ta jero sababbin shiga jam’iyyar hamayyar, daga ciki akwai; Ali Haruna Makoda, Tijjani Abdulkadir Jobe, Abdulmumin Jibrin, da Badamasi Ayuba.

A baya Legit.ng Hausa ta rahoto ficewar Abdulrahman Kawu Sumaila da Kabiru Alhassan Rurum.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Akwai Najib Abdussalam, Umar Maitsidau, Halliru Maigari, Hafizu Maidaji, Safiyanu Harbau, da Habiba Yandalla. Bayan haka akwai ‘yan majalisar dokoki 13.

2. Rikicin cikin gidan APC

Tun ba yau ba ake fama da rigimar cikin gida a APC na jihar Kano. Rikicin nan da uwar jam’iyya ta gagara shawo kan shi ya bata lamarin jam’iyya mai mulki.

A 2018 ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Umar Haruna Doguwa daga kujerar shugaban APC. A yau Doguwa ne shugaban NNPP a jihar Kano.

Kawo Abdullahi Abbas da aka yi da musamman zarcewan da ya yi a kan kujerarsa ya kawo rigima a APC. A dalilinsa ne aka samu kafuwar ‘yan tawaren G7.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Wasu daga cikin ‘yan G7 irinsu Ibrahim Shekarau da Tijjani Jobe sun koma NNPP, Mu’azu Magaji ya shiga PDP, wasunsu za su yaki tsagin Ganduje na APC a 2023.

Masu fashin baki na ganin sauya-shekar Ibrahim Shekarau daga APC za ta karfafi jam’iyyar NNPP.

Manyan NNPP
Jagororin NNPP na Kano a yau Hoto: @Mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

3. Karfa-karfa da kakaba ‘yan takara

Masu fashin baki su na ganin kakaba ‘yan takara da karfi da yaji ne ya sa Abdulmuminu Jibrin ya fice daga APC, ya zabi ya koma NNPP domin ya samu tikiti.

Shi ma Kawu Sumaila ya bar APC ne bayan ya fahimci ba zai samu takarar Sanatan Kano ta Kudu a 2023 ba. Alamu na nuna Gwamna na tare da Kabiru Gaya.

Ganin ba za su samu tikitin APC ba ya sa su Ali Makado suka tsallako zuwa bangaren Kwankwaso. Makado shi ne babban hadimin fadar gwamna.

4. Watsi da kudancin Kano

Baya ga irinsu Hon. Kawu Sumaila, Kabiru Alhasan Rurum da wasu manyan ‘yan siyasar kudancin jihar su na ganin ba a dauke su komai ba a tafiyar APC.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal ya tona ‘Dan Arewan da APC ta ke shirin ta tsaida takarar Shugaban kasa

Daga 1999 zuwa yau, kujerar gwamna ta na yawo ne tsakanin yankin Arewa zuwa tsakiyar Kano. Rabon da yankin su yi gwamna tun lokacin Kabiru Gaya a 1992.

Wannan ya sa aka yi ta ganin jiga-jigai daga wannan yanki su na shiga kwandon kayan dadi.

5. Matsalar Ganduje a gida

An samu mummunan rikici tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da ‘dan majalisarsa, Tijjani Jobe. Tun bayan zabe alakar ‘yan siyasan na yanki guda ta cabe.

Haka zalika Mai girma gwamnan ya yi ta samun sabani da Sanatansa, Barau Jibrin. A karshe dai Gwamnan ya yi sulhu da shi, amma har yau babu jituwa a shiyyar.

6. Rikicin shugabanci a PDP

Har zuwa yanzu ana ta shari’a a kotu a kan wanda zai jagoranci jam’iyyar PDP na reshen Kano. Ana zargin Shehu Wada Sagagi yana tare da su Rabiu Kwankwaso.

Sagagi ya karyata zargin da ake yi masa na alaka da tsohon gwamnan a boye. Ganin an rasa inda PDP ta sa gaba, mafi yawan ‘yan siyasan Kano su ke kaurace mata.

Kara karanta wannan

Akwai kallo a 2023: Za mu birkita lissafin duk wadanda suke raina mu - Jam’iyyar NNPP

Ko da PDP ta karbi wasu da suka bar Kwankwasiyya kamar Yunusa Dangwani, Yusuf Danbatta da mutane irinsu Mohammed Abacha da jagoran Win-Win, Muaz Magaji.

7. Karfin Kwankwasiyya a Kano

Jaridar ta ce babban abin da ya yi tasiri wajen karfin NNPP a jihar Kano shi ne tafiyar tsohon Gwamna Rabiu Musa Kwankwaso wanda aka sani da Kwankwasiyya.

Sanata Rabiu Kwankwaso yana da dinbin mutane musamman matasa da ke goyon bayan shi. Ficewarsa daga PDP ta karya jam’iyyar, sannan ta kuma tado da NNPP.

Legit.ng Hausa ta fahimci tsohon Ministan ya yi kokarin wajen jawo wasu daga cikin wadanda APC ta ke ji da su a lokacin da yake harin kujerar shugaban kasa a 2023.

Meyasa NNPP ta ke samun karbuwa?

Legit.ng Hausa tayi magana da Mahbub Ibrahim mai neman takarar ‘dan majalisar tarayya a Kano, ya shaida mana sirrin farin jinin jam’iyyarsu ta NNPP.

A cewar Injiniya Mahbub Ibrahim, ana rububin jam’iyyar ne saboda gaskiya da kaunar da talakawa ke yi wa jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Kwankwasiyya ta samu karuwa, shugaban yakin neman zaben Tinubu ya rungumi NNPP

Haka zalika ya ce yadda aka shigar da dinbin matasa cikin harkar siyasar ta taimakawa jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel