Guguwar NNPP na neman ratsa siyasar Kano, Shekarau da su Sumaila za su fice daga APC

Guguwar NNPP na neman ratsa siyasar Kano, Shekarau da su Sumaila za su fice daga APC

  • Watakila tsohon Gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP
  • Malam Shekarau ya fahimci zai iya rasa takarar Sanata a dalilin sababinsa da Abdullahi Ganduje
  • Shi ma Hon. Abdulrahman Kawu Sumaila mai neman Sanatan Kudancin Kano yana shirin barin APC

Abuja - Dinbin mutane sun fice ko sun kama hanyar ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki a jihar Kano, da yawa su na shiga NNPP mai alamun kayan marmari.

Jaridar Daily Nigerian ta fira da rahoto cewa tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau da Kawu Sumaila sun kammala shirye-shiryen watsi da jam’iyyar APC.

Rahoton da aka fitar a ranar Litinin ya bayyana cewa Sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau ya kira wani zama da makusantansa da ake kira majalisar Shura.

Kara karanta wannan

Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

A wajen wannan zama ne ake sa rai Shekarau zai shaidawa magoya bayansa inda ya dosa a siyasa.

Tsohon ‘dan majalisa kuma tsohon hadimin shugaban kasa, Kawu Sumaila da sauran wadanda suke ganin an yi masu ba daidai ba a APC za su shiga NNPP.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa Shekarau da Sumaila sun yi wani zama na musamman da jagoran NNPP na kasa, Rabiu Kwankwaso jiya a gidansa a Abuja.

Guguwar NNPP
Magoya bayan jam'iyyar NNPP Hoto: @mohd.saifullahi.9
Asali: Facebook

Dederi da Auduwa su na hanya?

Wata majiya ta shaida cewa Shekarau ya tattauna da manyan NNPP, zai shiga jam’iyyar tare da wasu ‘yan majalisar tarayya; Haruna Dederi da Nasiru Auduwa.

Dederi da Auduwa su na wakiltar mazabun Karaye/Rogo da Gabasawa/Gezawa a majalisar tarayya. Duk su na cikin wadanda aka samu sabani da su a APC.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Shekarau Ya Ƙi Bin Ganduje Zuwa Ganin Buhari a Abuja Bayan Gano Maƙarƙashiyar Da Aka Shirya Masa

Za a yaki Shekarau a APC?

Politics Digest ta ce uwar jam’iyya ta bukaci a bar duk wani tsohon gwamna da yake takarar Sanata ya koma kan kujerarsa a APC a 2023 ba tare da hamayya ba.

Amma a Kano, ana jin kishin-kishin cewa Bashir Garba Lado, A.A. Zaura da Ismail Ahmed sun yanki fam da nufin su gwabza da Shekarau a zaben fitar da gwani.

NNPP ta fara yin karfi

A karshen makon da ya wuce aka ji Abdulkadir Tijjani Jobe mai wakiltar Dawakin-Tofa/Tofa/Rimin Gado a majalisar tarayya ya bar APC zuwa NNPP.

Haka zalika ‘dan majalisar dokoki na yankin, Mohammed Butubutu ya bi Jobe zuwa NNPP mai adawa.

A ranar Juma'a ne aka ji yadda wasu daga cikin ‘yan majalisan dokoki na jihar Kano su ka sauya-sheka daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa NNPP.

Wata sanarwa da ake ikirarin ta fito daga Darektan yada labarai da hulda da jama’a na majalisar dokokin jihar Kano, Uba Abdullahi ya tabbatar da wannan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel