Muna maraba da kowa zuwa NNPP, inji Kwankwaso yayin da ake cigaba da tattaunawa da Shekarau

Muna maraba da kowa zuwa NNPP, inji Kwankwaso yayin da ake cigaba da tattaunawa da Shekarau

  • Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kofar shigowa jam'iyyar su a buɗe take ga kowa
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce sun kafa jam'iyyar NNPP ba ga makusanta kaɗai ba, kowa ya na da dama har da wanda ba su shiri
  • Bayanai masu karfi sun nuna cewa tattaunawa ta yi nisa na sauya shekar Shkarau zuwa NNPP

Kano - Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kofar shigowa jam'iyyar a bude take, har da mutanen da ba su ga maciji, Daily Trust ta rahoto.

Kwankwanso ya yi wannan furucin ne yayin da rahotanni ke nuna cewa wani tsohon gwamna a Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, da yan tawagarsa na shirin ficewa daga APC.

Haka zalika, tsohon kakakin majalisar dokokin Kano, Alhassan Rurum, wanda bai jima da barin APC ba, da tsohon ɗan majalisar tarayya, Kawu Sumaila, duk sun kammala shirin shiga NNPP.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso.
Muna maraba da kowa zuwa NNPP, inji Kwankwaso yayin da ake cigaba da tattaunawa da Shekarau Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Da yake jawabi a wani gidan Radiyo a Kano, Kwankwaso ya ce NNPP na bukatar karin mambobi kuma a shirye take ta karɓi duk wanda ya shirya shigowa a dama da shi.

Ya ce:

"Kamar yadda muka gina jam'iyyar nan muna bukatar mutane da yawa su shigo, waɗan da muka sani da waɗan da bama mu san su ba, har mutanen da muke da saɓanin fahinta da su, zamu so su shigo."
"Ba zamu killace jam'iyyar ga na kusa da mu kaɗai ba, hakan ba zai taimaki jam'iyyar ta faɗaɗa ba. Muna farin ciki yadda NNPP ke jan hankalin mutane, muna maraba da duk wanda ya shirya gyara Najeriya."
"Muna da shiri ga ƙasa, muna son ceto yan Najeriya daga ƙangin talauci, rashin tsaro, faɗuwar tattalin arziki yayin da muke shirin tunkarar babban zaɓen 2023."

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Kofar mu a buɗe take ga yan G7 inji Kwankwaso

Bugu da ƙari, Kwankwaso ya buɗe kofar shiga jam'iyyarsa ta NNPP ga yan tsagin G-7 ƙaraƙashin jagorancin sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau.

"Game da yan tsagin G7 waɗan da mutane ne yan asalin jihar mu ta Kano duk muna maraba da su zuwa NNPP," Inji shi.

Zamu kafa gwamnati a jihar Kano - Kwankwaso

Tsohon gwamnan ya ƙara da cewa a zaɓen 2023, jam'iyyar NNPP zata kafa gwamnati a jihar Kano domin canza abubuwan da aka ɓata.

"Kowane Bakano ba ya jin daɗin yadda abubuwa ke tafiya, abun takaici ne yadda aka lalata Kano cikin shekara 7 da suka shuɗe, zamu dawo da komai kan hanya da izinin Allah."

A wani labarin kuma Kotu ta ba da umarnin kama mataimakin Sufetan yan sanda na ƙasa da SP

Wata Kotu a Ogun ta umarci a tsare mataimakin Sufeta Janar (AIG) na shiyya ta 2 da Sufurtandan yan sanda a gidan gyaran Hali.

Kara karanta wannan

Wani Bam ya ƙara tashi mutane na tsaka da holewa a jihar Kogi, rayuka sun salwanta

Alkalin Kotun, Mai shari'a Ogunfowora, ya ɗauki wannan matakin ne bayan sun yi fatali da umarninsa, ya ce hakan raina sashin shari'a ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel