Kwankwasiyya ta samu karuwa, shugaban yakin neman zaben Tinubu ya rungumi NNPP

Kwankwasiyya ta samu karuwa, shugaban yakin neman zaben Tinubu ya rungumi NNPP

  • Manyan ‘yan jam’iyyar NNPP sun fito sun tarbi Rabiu Musa Kwankwaso a filin jirgin Malam Aminu Kano
  • Abdulmumin Jibrin ya koma NNPP, yana cikin wadanda aka gani wajen yi wa Kwankwaso maraba da zuwa
  • Tsohon ‘dan majalisar na Kiru da Bebeji ya shiga jam’iyyar adawar mai alamar kayan dadi ne bayan barin APC

Kano - Abdulmumin Jibrin wanda yana cikin manyan masu yi wa Bola Tinubu yakin zama shugaban Najeriya, ya shiga jam’iyyar hamayya ta NNPP.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tsohon ‘dan majalisar na yankin Kiru/Bebeji ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar NNPP a ranar Juma’a, 13 ga watan Mayu, 2022.

Hon. Abdulmumin Jibrin yana cikin wadanda aka gani a filin sauka da tashin jirgin saman Malam Aminu Kano wajen tarbar Sanata Rabiu Kwankwaso.

Tsohon Gwamnan na Kano ya dawo daga birnin tarayya Abuja tare da wasu manyan ‘yan siyasa da suka sauya-sheka kwanan nan daga APC zuwa NNPP.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

A wani bidiyo da gidan rediyon Premier radio 102.7 suka haska kai-tsaye, an ga zugar ta tarbi jagoran na tafiyar Kwankwasiyya watau Rabiu Kwankwaso.

An ga Jibrin tare da wasu jagororin NNPP na jihar Kano da suka hada da shugaban NNPP, Umar Haruna Doguwa dauke da kwando mai alamar kayan dadi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hon. Abdulmumin Jibrin
Hon. Abdulmumin Jibrin a NNPP Hoto: Ibraheemz01
Asali: Facebook

Injiniya Abba Kabiru Yusuf ya jagoranci ‘Yan NNPP da Kwankwasiyya wajen tarbar Madugun na su.

Na gaji da zama a APC - Jibrin

Hakan na zuwa ne kusan mako daya da aka ji ‘dan siyasar ya bada sanarwa ficewa daga APC mai mulki. A lokacin ya ce bayan sa’o'i 24 za a ji inda ya sa gaba.

Jaridar Daily Nigerian ta ce Jibrin ya zabi ya koma NNPP ne bayan ya yi zama na musamman da jagororin jam’iyyar hamayyar a Kano da kuma birnin tarayya.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

APC ta na cigaba da rasa ‘ya ‘yanta

Labarin sauya-shekar Jibrin na zuwa ne a lokacin da aka ji ‘dan majalisar Bagwai/Shanono, Hon. Ali Ibrahim Isa Ali Shanono ya bayyana ficewarsa daga APC.

Sauran wadanda suka fita daga APC zuwa NNPP daga jiya zuwa ranar Juma'a, sun hada da; Hon. Hafizu Sani Medaji, da Habiba Yardallah da Hon. Yakubu Ado.

Shekarau ya ki zama da Gawuna

A makon nan aka ji tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya ki bari su zauna da mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna a kan rikicin APC.

Gawuna ya nemi ya hadu da Sanatan na Kano ta tsakiya mai-ci, Malam Ibrahim Shekarau a gidansa domin a dinke baraka, amma haduwarsu ba ta yiwu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel