2023: Tambuwal ya tona ‘Dan Arewan da APC ta ke shirin ta tsaida takarar Shugaban kasa

2023: Tambuwal ya tona ‘Dan Arewan da APC ta ke shirin ta tsaida takarar Shugaban kasa

  • Ana kishin-kishin cewa Ahmad Ibrahim Lawan zai rikewa APC tuta a zaben shugaban Najeriya
  • Gwamna Aminu Waziru Tambuwal ya bayyana wannan da ya je yakin neman kuri’un ‘yan PDP
  • Tambuwal ya ce saboda za a ba Sanata Lawan takara ne APC ta yi gum a kan batun karba-karba

Kogi - Idan abubuwa suka cigaba da tafiya a haka, jam’iyyar APC mai mulki za ta tsaida Ahmad Lawan ne a matsayin ‘dan takarar kujerar shugaban kasa.

Jaridar This Day ta rahoto Gwamnan Sokoto, Aminu Waziru Tambuwal yana wannan magana.

Rt. Hon. Aminu Waziru Tambuwal ya ziyarci garin Lokoja a jihar Kogi domin samun goyon bayan masu zaben ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar adawar.

Gwamnan ya shaidawa ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP cewa sun gano dabarun da APC ta ke shirin yi, a cewarsa jam'iyyar na neman yin watsi da tsarin karba-karba.

Kara karanta wannan

Sakamakon umarnin da aka bada, mai ba Buhari shawara ya ajiye aiki domin neman Gwamna

Kamar yadda aka fitar da rahoton dazu, Aminu Waziru Tambuwal ya ce APC ta na sauraron wanda za a ba tutan takara a PDP kafin tayi zaben fitar da gwani.

Abin da Rt. Hon. Tambuwal ya fada

“Sannu a hankali, su na watsi da tsarin karba-karbarsu. Mun san dabarunsu. Su na so su ga yadda zaben fitar da gwaninmu zai kasance.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tambuwal
Gwamnan Sokoto, Aminu Waziru Tambuwal Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

“Su na so sai mun tsaida ‘dan takara a ranar 28 da 29 ga watan Mayu, kafin su yanke hukuncin wanene wanda zai zama ‘dan takararsu.”
“Ku duba shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya yi shiru game da batun karba-karba, saboda sun yi shirin tsaida Sanata Ahmad Lawan ne.”

Tambuwal ya caccaki mulkin APC

‘Dan takarar shugaban kasar na PDP ya soki gwamnatin APC, ya ce idan jam’iyyar ta zarce a mulki za a cigaba da ganin tsare-tsaren Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Magana biyu: Bayan sun nuna su na goyon bayan Tinubu, ‘Ya ‘yan APC sun ce su na tare da Amaechi

A cewar tsohon shugaban majalisar wakilan, lamarin tsaro ya tabarbare a gwamnatin APC mai-ci. Tambuwal ya ce muddin APC ta zarce, abin zai fi muni.

Ku yafe mani abin da ya faru a 2014

Har ila yau, Gwamna Tambuwal ya nemi afuwar ‘yan PDP na sauya-sheka da marawa APC baya da ya yi wajen kifar da mulkin Dr. Goodluck Jonathan a 2015.

'Dan siyasar ya yi kira ga 'yan PDP su ba shi kuri'unsu domin a maida APC tarihi a zabe mai zuwa.

2023: APC ta na tsoron 'Dan Arewa?

Rahoton da mu ka fitar a makon nan ya shaida cewa APC ta ki ayyana yankin da zai fito da ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, ta na jiran motsin PDP.

Jam’iyya mai mulki ta shiga rububi ne saboda tsoron PDP za ta iya tsaida irinsu Atiku Abubakar. Tsoron APC shi ne a karbe mata kuri'un yankin Arewa a 2023.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel