Akwai kallo a 2023: Za mu birkita lissafin duk wadanda suke raina mu Inji Jam’iyyar NNPP

Akwai kallo a 2023: Za mu birkita lissafin duk wadanda suke raina mu Inji Jam’iyyar NNPP

  • Shugaban jam’iyyar adawa ta NNPP na kasa ya sha alwashin za su ba mutane mamaki a filin zabe
  • Rufai Ahmed Alkali ya shaidawa Duniya cewa su na kokarin hambarar da APC da PDP a Najeriya
  • Farfesa Alkali ya ce idan NNPP ta yi nasarar kafa gwamnati, za ta magance matsalolin kasar nan

Abuja - Shugaban jam’iyyar hamayya ta NNPP, Rufai Ahmed Alkali, ya ce jam’iyyarsu da ake yi wa lakabi da mai kayan marmari za ta ba mutane mamaki.

Daily Trust ta ce Farfesa Rufai Ahmed Alkali ya bayyana wannan ne a lokacin da yake zantawa da wasu manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Rufai Ahmed Alkali ya ce shugabannin NNPP sun fara kokarin ganin yadda jam’iyyar adawar za ta shiga ko ina a kasar nan, ta tallata kanta ga al’umma.

Kara karanta wannan

Matashi ‘Dan shekara 38 ya fito zai jarraba sa'a a takarar Shugaban kasa a zaben 2023

Farfesan ya shaidawa ‘yan jarida cewa jam’iyyar NNPP za ta ceto mutanen Najeriya daga hannun manyan tsofaffin jam’iyyun nan biyu watau PDP da APC.

Shugaban NNPP na kasa ya zargi jam’iyyun na PDP da APC da cewa ba su da manufa da hangen nesa. Jaridar Tribune ta fitar da rahoton nan a ranar Asabar.

Da yake magana a ranar Asabar, Farfesa Alkali ya ce sun fara neman yadda za su fito da ‘yan takarar da za su tsaya mata a zabe mai zuwa da za ayi a 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam’iyyar NNPP
Magoya bayan Jam’iyyar NNPP a Kano Hoto: New-Nigeria-Peoples-Party-NNPP-Kano-State
Asali: Facebook

Mun fara shirin zaben 2023 - NNPP

“Za a fara wannan ne a ranar Litinin 16 ga watan Mayu 2022 ta hanyar tantance masu neman takarar majalisar dokokin jiha.”
“Za a cigaba da wannan har zuwa zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa da za ayi a garin Abuja a ranar 2 ga watan Yunin 2022.”

Kara karanta wannan

Magana biyu: Bayan sun nuna su na goyon bayan Tinubu, ‘Ya ‘yan APC sun ce su na tare da Amaechi

- Rufai Ahmed Alkali

Har ila yau, Alkali ya ce jam’iyyarsu ta NNPP ta dauki matakan da za su hana a samu rigima wajen zabukan tsaida ‘yan takara da za ayi a watan Yuni mai zuwa.

“Bari in tabbatar maku da wannan a bainar jama’a, a zaben 2023, NNPP za ta ba mutane mamaki a filin zabe.”
“Kuma da yardar Ubangiji idan mu ka kafa gwamnati, za mu shawo kan matsalar tsaro, mu dawo da kimar Naira.”
“Za mu samar da ayyukan yi ga miliyoyin matasa, mu ba mata matsayinsu a gwamnati, mu babbako da masana’antu.”

- Rufai Ahmed Alkali

Rufai Ahmed Alkali ya yi alkawari gwamnatin NNPP za ta yi aiki da doka, tare da tafiya da kowa.

Amaechi ne ko Tinubu a APC?

Dazu aka ji labari Nasir El-Rufai ya ayyana Rotimi Amaechi a matsayin magajin Muhammadu Buhari duk da ya yi wa Bola Tinubu alkawarin mara masa baya a APC

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Mai girma Gwamna El-Rufai ya nuna babu ruwansa da zabin 'dan takara, domin zai goyi bayan duk wanda ‘yan jam’iyyar APC na Kaduna su ke so ne da takara a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel