Gidan Yari Ne Muhallin Gawuna Da Garo A Duniyar Da Aka Cigaba, Farfesa Hafizu

Gidan Yari Ne Muhallin Gawuna Da Garo A Duniyar Da Aka Cigaba, Farfesa Hafizu

  • Farfesa Hafiz Abubakar, tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano ya ce a kasa da aka cigaba ya kamata Gawuna da Murtala Garo suna gidan yari
  • Hafiz ya furta hakan ne cikin wani faifan bidiyo a wurin wata lakca da aka yi a Kano yana mai nuna takaicinsa game da yadda wadanda suka kawo cikas ga zabe za su zama yan takarar gwamna
  • Ya kuma bayyana cewa ba su takarar gwamna da mataimakin gwamna tamkar wata sakayya ne aka musu duk da cewa sun aikata abin da ya saba wa doka

Kano - Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano, Hafiz Abubakar, ya ce mataimakin gwamnan Kano mai ci kuma ɗan takarar gwamna na APC a zaɓen 2023, ya kamata yana gidan yari tare da abokin takararsa, Murtala Garo, rahoton Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado

Mr Abubakar, Farfesa a ɓangaren nazarin sinadarai masu gina jiki ya furta hakan cikin wani faifan bidiyo da ake kyautata zaton an naɗa a wurin lakca a Kano.

Gidan Yari Ne Muhallin Gawuna Da Garo A Duniyar Da Aka Cigaba, Farfesa Hafizu
Farfesa Hafizu: Gidan Yari Ne Muhallin Gawuna Da Garo A Wurin Da Aka Cigaba. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Nigerian ta rahoto cewa Gawuna da Garo sun kawo cikas wurin tattara sakamakon zabe a ƙaramar hukumar Nassarawa a zaɓen gwamna na 2019 a lokacin da dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf kan gaba da ƙuri'u da dama.

Lamarin ya tursasa aka bayyana zaben a matsayin 'inconclusive' sannan daga baya da aka kammala zaben gwamna Abdullahi Ganduje ya yi nasara a cewar INEC.

A wani abu da ya yi kama da sakayya, Ganduje ya zabi Gawuna da Garo a matsayin wadanda ya ke son su yi takarar gwamna a APC a 2023.

An yi fostoci masu ɗauke da rubutun "Dakarun Inconclusive", a wani abin da ya yi kama da yin jinjina ga mutanen biyu kan yadda suka janyo INEC ta ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba lokacin.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Farfesa Abubakar ya yi alla wadai da fostocin, yana mai cewa ya kamata yan takarar gwamnan da mataimakinsa su kasance a gidan gari idan da a garin da doka ke aiki suka yi hakan.

"Na bada misali da Kano a yau. A yau a Kano, muna da allunan talla da ke jinjina wa mutanen da suka janyo aka ayyana zabe a matsayin Inconclusive a 2019, wanda bidiyon su ya bazu a kasa, suna zuwa wurin zabe don kawo cikas da sace kuri'a.
"Yan takarar na gwamna da mataimakinsa kamata ya yi suna gidan yari a kasa da doka ke aiki. A yau, sune yan takarar gwamna a Kano a zaɓen 2023. Har ma ana yin fostoci don jinjina musu. Wadanda suka janyo Inconclusive sun zama jarumai!.
"Zan ƙyalle mu mu yanke hukunci game da inda muke a siyasa a yau, zan dawo bayan lakcan, nagode," ya ƙara da cewa.

Mataimakin Kakakin Majalisar Kano Ya Fice Daga APC, Ya Bi Kwankwaso Jam'iyyar NNPP

Kara karanta wannan

Magajin Aminu Kano: Bayan Lukman Labarina, Wani Jarumin Kannywood ya fito takara a Kano, ya karɓi Fom

A wani rahoton, mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam'iyyar All Progressives Congress, APC ya koma New Nigeria People's Party, NNPP, rahoton Daily Nigerian.

Mr Massu, ɗan siyasa daga mazabar Kano ta Kudu, ya sanar da ficewarsa daga APC cikin wata wasika da ya aike wa shugaban jam'iyyar na APC a mazabar Massu.

Ɗan majalisar ya bayyana rikice-rikicen jam'iyyar da rashin demokradiyya ta cikin gida a matsayin dalilin ficewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel