Siyasar Kano: Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado

Siyasar Kano: Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado

  • Tsohon sanata mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya, Sanata Basheer Lado ya yi martani a kan fitowarsa takarar kujerar da ya bari
  • Lado ya karyata zargin cewa gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje ne ya nemi ya fito takarar kujerar kamar yadda Shekarau ya fadi
  • Ya ce ya fito ne don ra'ayin kansa da kuma zawarcinsa da al'ummar Kano musamman na yankin suka yi

Kano - Tsohon sanata mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya, Sanata Basheer Garba Mohammed (Lado), ya bayyana cewa ba za a iya yi masa makarkashiya don lalata kudirinsa na komawa majalisar dattawa ba a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, Sanata Lado ya nesanta kansa daga rahoton kwanan nan kan wani furuci da aka alakanta da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gidan Yari Ne Muhallin Gawuna Da Garo A Duniyar Da Aka Cigaba, Farfesa Hafizu

Siyasar Kano: Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado
Siyasar Kano: Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado Hoto: PM News
Asali: Facebook

Ya ce:

“Na yi matukar damuwa da karanta wani labari a shafukan politicsdigest.ng da alfijir.com.ng a ranar 9 ga watan Mayun 2022 da wasu kafofin watsa labarai da dama, wanda ya nakalto Malam Ibrahim Shekarau yana cewa Mai Girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umurce ni da na yi takarar kujerar sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya.
“A ka’ida ba na shiga kowace irin cece-ku-ce na siyasa da ake kwancewa juna zani a kasuwa kuma da na gwammaci na yi shiru na mutunci amma ya zama dole in mayar da martani don kada wasu su yarda da zargin.”

Sanata Lado ya rantse cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai sanya shi yankan fom din takara ba, yana mai cewa duk labarin kanzon kurege ne kuma kage ne don jan hankalin jama’a da kuma yunkurin bata sunansa da na Ganduje.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Ya yi bayanin cewa kudirinsa na son komawa majalisar ya kasance ne sakamakon neman hakan da magoya bayansa suka yi da kuma yadda jama’ar jihar Kano masu karamci ke zawarcinsa musamman ma al’ummar Kano ta tsakiya suka yi.

Ya ce:

“Kan lamarin, kawai na sanar da mai girma, Dr. Umar Ganduje, aniyata ta son takara bayan na yanke hukunci kuma na sanar da shi cewa na siya fom din bayan na aikata hakan ba wai kafin na yi ba.”

2023: APC ta tara sama da biliyan N29 daga siyar da fom din takara

A wani labari na daban, mun ji cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tara kudi fiye da naira biliyan 29 daga siyar da fom din takarar kujeru daban-daban a babban zaben 2023.

Jam’iyyar mai mulki ta tsawwala fom dinta na takarar shugaban kasa zuwa naira miliyan 100, na gwamna naira miliyan 50, na sanata naira miliyan 20 sannan nay an majalisar wakilai naira miliyan 10.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

Daily Trust ta rahoto cewa babban sakataren tsare-tsare na jam’iyyar ta kasa, Sulaiman Argungu, ya fada ma manema labarai a Abuja cewa yan takara 145 ne suka siyi tikitin takarar gwamna, 352 suka siya don takarar zaben fidda yan takarar sanata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel