Jarumin Kannywood, Ali Rabiu Ali, ya fito takarar ɗan majalisar tarayya a 2023

Jarumin Kannywood, Ali Rabiu Ali, ya fito takarar ɗan majalisar tarayya a 2023

  • Jarumi, Furodusa kuma Darakta a masana'antar Kannywood, Ali Rabiu Ali, ya tsaya takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Dala a Kano
  • Jarumin, wanda ya bayyana kansa da jikan Malam Aminu Kano, ya ce ya shirya ɗorawa daga inda kakansa ya tsaya
  • Ya ce abokai ne suka ja ra'ayinsa na ya fito takara domin ya taimakawa talakawa ganin zuciyarsa ta na da kyau

Kano - Jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa Kannywood, Ali Rabiu Ali, ya tsaya takarar ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar mazaɓar Dala ta jihar Kano.

A wata Fasta da jarumin ya saki a shafinsa na Instagram, Ali wanda aka fi sani da Daddy ya nuna cewa yana fatan ya zama magajin Malam Aminu Kano.

Ali wanda Furudusa ne kuma Darakta a Kannywood a ya wallafa Hotonsa ɗauke da Fom ɗin takara karkashin inuwar jam'iyyar PRP.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

Jarumi Ali Rabiu Ali.
Jarumin Kannywood, Ali Rabiu Ali, ya fito takarar ɗan majalisar tarayya a 2023 Hoto: @alirabiuali_daddy
Asali: Instagram

Ya ce ya ɗaɗe yana ciwom yadda ake jagoranci tun daga matakin ƙasa, jihohi, kananan hukumomi da ma'aikatun gwamnati domin shugabanni ba ta talakawa suke ba, manufar kansu kaɗai suka tasa a gaba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa abokanai da yan uwa sun jima suka rokon ya fito takara domin taimaka wa Talatkawa saboda sun san abin da ke cikin zuciyarsa amma yace bai yarda ba ganin ba zai iya shiga cikin yan siyasa ba.

Ni jikan Aminu Kano ne - Ali

Haka nan Jatumin ya bayyana cewa shi jikan Malam Aminu Kano ne kasancewar shi ne wanda ya haifi mahaifiyarsa, sai dai a bayaninsa ya ce yan siyasar yanzu sun bar turbar da kakansa ya ɗora su.

Ali ya ce:

"A sani na yan siyasar zamanin nan mafi yawa sun bar kan aƙidar Kakana Malma Aminu Kano ta ɓangaren kokarin kwato hakkin talakawa da rike amana, kula da lafiya, ilimi da walwalar talakawa."

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Zan ɗora daga inda kakana ya tsaya

Bayan haka, Daddy ya ƙara da cewa ya yi kudirin tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Dala mahaifarsa karkashin inuwar PRP da Malam Aminu Kano ya kafa.

"Ina fatan ɗorawa daga inda ya tsaya da yardar Allah kuma da karfin ikon Allah domin na yi bakin kwarkwardo a ɓangaren wakilci. Idan zan zama Alkairi ga al'ummar Dala Allah ya sani."

A wani labarin kuma Kannywood: Jarumi Lukman na Shirin Labarina ya fito takarar siyasa a jihar Kano

Yayin da zaɓen 2023 ke ƙara ƙaratowa, yan Najeriya dake da niyyar tsayawa takara na cigaba da faɗa wa duniya aniyarsu.

A masana'antar Kannywood, Jarumi Lukman na Labari na ya bayyana tsayawa takarar ɗan majalisar tarayya daga Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel