Rikicin APC: Gwamnoni masu dabi'ar 'yan Yahoo, Yahoo ne kadai ke tare da Buni, Akeredolu

Rikicin APC: Gwamnoni masu dabi'ar 'yan Yahoo, Yahoo ne kadai ke tare da Buni, Akeredolu

  • Gwamnan jihar Ondo ya siffanta takwarorinsa dake goyon bayan Gwamna Mai Mala Buni a matsayin gwamnoni 'yan damfara
  • An samu sabanin ra'ayi tsakanin Gwamna Nasir El-Rufai da David Umahi na jihar Ebonyi a kan lamarin Gwamna Buni
  • Yayin da Umahi ya ce har yanzu Buni ne ke da alhakin kula da jam'iyyar, El-Rufai cewa yayi Buni ba zai taba dawowa matsayin shugaban jam'iyyar APC na rikon kwarya ba

Gwamna Rotimi Akwredolu na jihar Ondo, ya siffanta takwarorinsa dake goyon bayan Mai Mala Buni a matsayin "Yan damfara, gwamnoni 'yan damfara."

An samu hatsaniya tsakanin shugabannin gwamnonin APC, tun lokacin da Abubakar Bello na jihar Neja ya amshi mulkin shugaban kwamitin rukon kwaryar jam'iyyar APC (CECPC), Daily Trust ta ruwaito hakan.

Rikicin APC: Gwamnoni masu dabi'ar 'yan Yahoo, Yahoo ne kadai ke tare da Buni, Akeredolu
Rikicin APC: Gwamnoni masu dabi'ar 'yan Yahoo, Yahoo ne kadai ke tare da Buni, Akeredolu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar Laraba, gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna da gwamna David Umahi na jihar Ebonyi sun samu sabanin ra'ayi a kan lamarin Buni, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mai Mala bai bani wata wasika ba: Gwamna Neja ya yi martani mai zafi

Yayin da Umahi ya ce har yanzu Buni ne ke da alhakin kula da jam'iyyar, shi kuma El-Rufai ya ce ba zai taba dawowa matsayin shugaban jam'iyyar APC ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A wata takarda mai taken " Buni, Bakar kafa mai cika aljihu, a zauren mulki wanda ke da burin ja-in ja da ra'ayin shugaban kasa", Akeredolu ya ce jam'iyya mai mulki ta rayu a kan "tsira daga kokarin juyin mulkin da azzalumin shugaba, kuma mai neman mulki ido rufe ta hanyan amfani da dabarbarun zamani wajen kange wasu."
"Ba shakka, tsayayyan shugabanci, gaskiya da rikon amanan da shugaban kasa ya kafa misali dashi, wanda yayi jagoranci ya taimaka wajen haifar da jam'iyyar APC da bata cancancin goyon bayan da jinjina kadan daga dukkan masu rike da mukamanta ba.
"Samar da kwamitin rikon kwarya (CECPC) na APC ya wuce a yi kira zuwa ga aiki. Aiki ne da ya zama wajibi kan da, sannan da fadada dokoki a wannan jam'iyyar tamu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Wasikar Mai Mala Buni ta karyata kalaman Nasir El-Rufa'i

"Sai dai, hargitsi da matsalolin dake faruwa cikin jam'iyyar mu a wasu watanni da suka wuce, musamman karkashin mulkin da bai dade da wucewa ba, yana nuna babban tozarci karara. Ba tare da tabbatar da samar da bayanai sannannu ga masu rike da mukamai ba, tafarkin da gwamna Mai Mala Buni ya dauka daga baya, wanda shi ne shugaban CECPC mai murabus, tare da wasu mutanen jam'iyyar, babu shakka abun taikaci ne da rashin kyautawa ga jam'iyyar mu. Wannan labari ne mai bai ban bakin ciki.
"Ba tare da kasa a gwuiwa ba, gwarzonta da jajircewa gami da hazakar nagarta na dalilin da yawancin gwamnonin APC suka kwatanta zai cigaba da zama abun ala sambarka.
"Abun burgewa shi ne, hanzarin martani da daukar mataki da shugaban kasa yayi, ba kadan ba, ya tseratar da jam'iyyar mu daga cin diddigen ta da wasu 'yan jam'iyyar ke yi. Hakika mun tsira daga kokarin juyin mulkin da azzalumin shugaba, kuma mai neman mulki ido rufe ta hanyan amfani da dabarbarun zamani wajen kange wasu."

Kara karanta wannan

Yadda Lauyoyin Mala Buni suka shirya makarkashiya domin yakar APC inji El-Rufai

Asali: Legit.ng

Online view pixel