Tsohon Kwamishina, Hadimin gwamna da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC

Tsohon Kwamishina, Hadimin gwamna da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC

  • Tsohon kwamishina, tsohon hadimin gwamna a lokacin mulkin PDP a Gombe sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC
  • Manyan jiga-jigan sun bayyana cewa kyakkyawan jagorancin gwamna Inuwa Yahaya ne ya jawo hankalisu ga APC
  • Sun tabbatar da cewa za su ba da gudummuwar da ake bukata wajen cigaban jihar Gombe da APC

Gombe - Manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka yi aiki a gwamnatin tsohon gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, sun sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Leadership ta rahoto cewa manyan mutanen da suka sauya shekan sun haɗa da, tsohon kwamishina, Babagoro Hashidu, da tsohon mashawarci na musamman, Alhaji Maigari Malala.

Kazalika sun koma APC tare da fitaccen ɗan siyasa kuma mai faɗa aji a siyasar PDP ta karamar hukumar Kwami, Alhaji Kari Daba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, tsohon ministan Buhari: Jerin yan siyasar da suka kafa sabuwar kungiyar siyasa

Tutar jam'iyyar APC
Tsohon Kwamishina, Hadimin gwamna da wasu jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Fitattun yan siyasan guda uku sun ziyarci gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, inda suka tabbatar da mubaya'ar su kuma suka shigar da gaisuwar girma.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa suka fice daga PDP suka koma APC?

Hashidu ya bayyana cewa ya ga dacewar komawa APC ne saboda nasararo masu ɗumbin yawa da gwamnatin APC ta cimma wa cikin ƙasa shekaru uku karkashin gwamna Inuwa Yahaya.

Tsohon kwamishinan ya ce:

"Lokacin da muka bar gadon mulki a 2019, mutane na jiran ganin jihar mu ta gaza. Amma bisa dace sai muka samu hazikin gwamna, wanda karkashin mulkinsa Gombe ta zarce inda ake tsammani."
"Kowa shaida ne ya ga manyan ayyukan da aka kammala karkashin gwamna Inuwa Yahaya, irin waɗan nan ayyukan raya ƙasa ne suka jawo hankali na na shigo APC."

A bangarensa, tsohon hadimin gwamna, Honorabul Maigari ya ce siyasa na nufin kawo wa al'umma cigaba kuma abin da gwamna Inuwa ya maida hankali kenan.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnan PDP ya sallami shugaban ma'aikatan fadar gwamnati daga aiki

"Saboda haka ba zamu bari mu zama karfen kafa ga kyakkyawan goben jihar mu ba don wata manufa ta ƙashin kan mu."

Zamu cigaba da ba da gudummuwa - Masu sauya sheka

Sabbin mambobin APC sun tabbatar da cewa za su cigaba da goyon bayan shirye-shirye da tsarin gwamnatin Inuwa Yahaya da kuma cigaban APC.

Masu sauya shekan sun samu ganin gwamna ne bisa jagorancin jigon APC a Gombe ta arewa, Alhaji Sani Jamare.

A wani labarin na daban kuma Manyan jiga-jigan APC da Mambobi sama da 5,000 sun sauya sheƙa zuwa PDP a jiha daya

Yayin da jam'iyyun siyasa ke shirin zaben 2023 dake tafe, Jam'iyyar PDP ta yi manyan kamu a jihar Bayelsa ranar Talata.

Wasu jiga-jigan APC da kuma dubbannin mambobin jam'iyyar sun sauya sheka zuwa PDP a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel