Gwamnan APC Ya Bayyana Wanda Zai Zaba Wa APC Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023

Gwamnan APC Ya Bayyana Wanda Zai Zaba Wa APC Dan Takarar Shugaban Kasa a 2023

  • Farfesa Ben Ayade, gwamnan Jihar Cross Rivers ya bayyana cewa ya yi imanin Shugaba Buhari ne zai zaba wa APC dan takarar da zai gaje shi
  • Ayade ya bayyana hakan ne yayin hira da aka yi da shi a ranar Juma'a yana mai cewa ya yi imanin Buhari zai zaba wa kasar wanda zai zama alheri
  • Ayade ya kuma ce zai goyi bayan duk wanda jam'iyya ta tsayar ko da Bola Tinubu ne ko Yemi Osinbajo ko kuma waninsu tunda zai jam'iyya ce ke gaban kowa

Gwamnan Jihar Cross Rivers, Farfesa Ben Ayade, ya ce ya yi imanin Shugaba Muhammadu Buhari zai yi zabi na gari yayin zaben wanda zai karbi mulki daga hannunsa a 2023.

A cewar Ayade, Buhari zai 'yi abin da ya fi zama alheri ga kasa' ya shawarci jam'iyyar All Progressives Congress, APC, game da wanda ya kamata a gaje shi, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

2023: Dalilai 2 da suka sa Farfesa Osinbajo ba zai yi takara da Bola Tinubu ba - Jigon APC

Buhari zai zabi dan takarar APC da zai gaje shi, Gwamna Ayade
Buhari ne zai zaba wa APC wanda zai gaje shi, Ayade. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Buhari zai yi wa Najeriya zabi na gari, Ayade

A hirar da ya yi da BBC Pidgin a ranar Juma'a, Ayade ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na yi imanin Buhari zai yi abin da ya dace da kasar nan. Iya sani na, Buhari shine wanda zai zaba wa APC wanda zai gaje shi. Idan ya ga cewa Osinbajo da suka yi aiki tare shekaru takwas ya dace, zan goyi bayansa. Mutumin kirki ne mai adalci. Hakan yasa za ka gane shi na kowa ne."

Tinubu bai yi laifi ba da ya fito takara, ya taimakawa Buhari sosai

Da aka masa tambaya game da fitowa takarar jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, Ayade ya ce yana da damar fitowa takarar musamman idan aka duba irin rawar da ya taka wurin nasarar Buhari.

Kara karanta wannan

Kotu ta aike ɗan gani-kashenin Atiku Abubakar gidan yari kan zagin Lamiɗon Adamawa

Ya ce:

"Dukkan masu fitowa daga kudu suna da ikon yin hakan. Wasu za su sake fitowa. Idan ka tambaye ni, zan ce Tinubu ya yi dai-dai da ya fito, saboda ya taka rawar gani wurin tabbatar da nasarar Buhari. Mutum irinsa zai yi tunanin fitowa takara tunda muna maganan mulki ya koma kudu."

Zan goyi bayan duk wanda jam'iyya ta tsayar

Sai dai, Ayade ya ce yana jira ne jam'iyya ta yi lissafi ta yanke shawara, kuma zai goyi bayan abin da ta yanke ko da wanene ta zaba.

A cewarsa:

"Mu yan gida daya ne. Su za su yi lissafi su fito da dan takara daya. Zai yiwu kana barci a gidan ka, sai ka ji sun kira ka sun tada ka daga barcin sun fada maka cewa kai ne aka zabe."

Buhari: Na Ji Daɗin Yadda Masu Hannu Da Shuni Suka Gane Cewa Canja Najeriya Ba Aikin Mutum Ɗaya Bane

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jamhuriyar Benin ta yanke sake tsare Sunday Igboho na tsawon watanni

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya yi farin cikin sanin cewa kusoshin Najeriya sun gane cewa canja kasar nan aikin kowa ne, The Cable ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana a wata takarda, Buhari ya yi wannan furucin ne a ranar Lahadi a wata liyafa ta girmama shugabannin kwamitin kasuwanci, siyasa, kafafen watsa labarai da sauran ma’aikata.

Dama a watan Janairun 2021 The Cable ta bayyana yadda Buhari ya zargi masu fada a jin kasar nan da kawo cikas ga gwamnatin sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel