Tsohuwar hadimar gwamnan APC da mambobi sama da 100,000 sun sauya sheka zuwa PDP a wannan Jihar

Tsohuwar hadimar gwamnan APC da mambobi sama da 100,000 sun sauya sheka zuwa PDP a wannan Jihar

  • Manyan jiga-jigan siyasa a jihar Ebonyi tare da dubbannin magoya baya sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP
  • Tsohuwar hadima ga gwamna Umahi na APC tare da ɗaruruwan mambobi sun koma PDP
  • Shugaban PDP na jihar Ebonyi yace tsintsiyar da ka kirkira domin share datti ba ta iya komai a halin yanzu

Ebonyi - Mambobi da magoya baya na jam'iyyar APC da ANN sama da 100,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a jihar Ebonyi.

Punch ta rahoto cewa daga cikin waɗan da suka sauya sheka har da mataimakin shugaban jam'iyyar ANN ta ƙasa (yankin kudu maso gabas), Mista Lazarus Eze, da tsohuwar hadimar gwamna Umahi na jihar Ebonyi, Martha Nwankwo.

APC zuwa PDP
Tsohuwar hadimar gwamnan APC da mambobi sama da 100,000 sun sauya sheka zuwa PDP a wannan Jihar Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Da yake karban masu sauya sheka a Ugwulangwu, karamar hukumar Ohaozara, shugaban PDP na jiha, mista Tochukwu Okorie, yace sun ɗauki matakin dawowa PDP ne saboda abubuwa sun lalace a jam'iyyun su.

Kara karanta wannan

Zamfara APC: Dan uwan Yari ya koma tsagin Matawalle, ya faɗi lokacin da Yari zai biyo bayansa

The Nation ta rahoto shi yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A yau muna tare da tsohuwar shugabar cibiyar Ohaozara East Development ta jam'iyyar APC domin ta bayyana komawarta PDP da sauran yan tawagarta."
"Tsintsiyar da aka yi domin share datti, yanzun ta kasa katabus, dattin ma takasa sharewa."

PDP ta lakume baki ɗaya jam'iyyar ANN a Ebonyi

Haka nan kuma shugaban PDP ya bayyana cewa jam'iyyar ANN reshen jihar Ebonyi ta koma cikin PDP baki ɗayanta.

"Ina amfani da wannan damar na gayyaci Lazarus Eze, tsohon mataimakin shugaban ANN na ƙasa, domin ya sanar muku da watsewar ANN a baki ɗaya yankin arewa ta gabas, zuwa PDP."
"Dukkan waɗan da ke cikin ANN kafin yanzu sun zo nan ne domin bayyana sauya shekar su zuwa jam'iyyar PDP."

Sama da mutum 100,000 sun koma PDP

Kara karanta wannan

Jami'an hukumar NSCDC guda 7 sun mutu a bakin aiki a jihar Neja

A nasa jawabin Eze ya bayyana cewa sun ɗauki matakin komawa PDP tare da mambobin ANN sama da 100,000 saboda bara gurbin dake zuwa su bata musu suna kuma su fice daga jam'iyyar.

A wani labarin kuma Dan uwan tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul'aziz Yari, yace ba zai yuwu yana ganin gaskiya ya guje mata ba, ya koma tsagin APC na gwamna Matawalle.

Turaki Abubakar, yace duk da Yari ɗan uwansa ne, amma abin takaici ne ya ƙi amince wa da zahirin gaskiya a jagorancin APC reshen jihar Zamfara.

Jigon APC a Zamfara ya kuma gargaɗi ɗan uwansa da cewa ya daina ruduwa da mutanen dake tare da shi, domin wata rana zasu rusa siyasarsa baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel