Jerin jam'iyyu 6 da zasu fafata a zaben kananan hukumomin wannan jihar, babu PDP a ciki

Jerin jam'iyyu 6 da zasu fafata a zaben kananan hukumomin wannan jihar, babu PDP a ciki

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Ekiti ta bayyana sunayen jam'iyyu 6 da zasu fafata a zaɓen kananan hukumomi dake tafe
  • Sai dai ga dukkan alamu, babu babbar jam'iyyar hamayya PDP a cikin jerin sunayen da hukumar SIEC ta fitar ranar Talata
  • Kwamishinan yan sandan jihar, Mr. Tunde Mobayo, ya gargaɗi masu tada kayar baya kada su shiga harkokin zaben dake tafe

Ekiti - Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Ekiti, (SIEC), Justice Jide Aladejana, yace jam'iyyun siyasa 6 ne kacal zasu fafata a zaɓen kananan hukumomin jihar.

Dailytrust ta ruwaito cewa hukumar SIEC ta shirya gudanar da zaɓen kananan hukumomi a jihar Ekiti ranar 4 ga watan Disamba, 2021.

Akwatin zabe
Jerin jam'iyyu 6 da zasu fafata a zaben kananan hukumomin wannan jihar, babu PDP a ciki Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban hukumar zaben ya bayyana sunayen jam'iyyun kamar haka:

Kara karanta wannan

Rikici tsakanin jiga-jigan APC ya barke bayan an saka ranar zaben sabbin shugabannin jam'iyya

"Jam'iyyar All Progressives Congress(APC), jam'iyyar Young Progressives Party (YPP), Jam'iyyar AA, jam'iyyar PRM da kuma jam'iyyar ADC."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane shiri hukumar zaben ta yi?

Aladejana yace hukumarsa zata gudanar da zaben ciyamomi da na kansiloli a kananan hukumomi 16 da aka sani a doka, da kuma sabbin yankuna 19 da a ka kirkira karkashin (LCDA).

Bugu da kari, ya tabbatar da cewa hukumarsu da kuma hukumomin tsaro sun kammala duk wasu shirye-shirye domin gudanar da sahihin zabe.

A cewarsa babu wanda za'a amince ya gurgunta namijin kokarin gwamnati na tabbatar da tsarin shugabanci a mataki na uku.

Aladejana ya bayyana haka ne ranar Talata a Ado Ekiti, yayin da yake ganawa da shugabannin jam'iyyun siyasa kan zaben dake tafe, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Wane shiri jami'an tsaro suka yi?

A nasu ɓangaren, rundunar yan sanda reshen jihar Ekiti, ta bayyana cewa ba zata bar wasu masu mummunan nufi su tada hankali ba yayin zaben.

Kara karanta wannan

Nasrun minallah: Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno

Kwamishinan yan sanda na jihar, Mr. Tunde Mobayo, ya gargaɗi duk masu shirin tada hargitsi kada su yi kuskuren zuwa wurin zaɓe.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Ganduje ya yi magana kan shirin gwamnatinsa na tube Shekarau daga sarautan 'Sardaunan Kano'

Idan baku manta ba, manyan jiga-jigan APC biyu sun fara taƙaddama da juna a lokacin gangamin taron jam'iyya na jihar Kano.

Yayin da tsagin gwamna Ganduje ya zaɓi Abdullahi Abbas a matsayin shugaba, shi kuma Shekarau ya bayyana Alhaji Haruna Danzago a matsyain shugaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel